Masarautar Kasar Saudiyya ta sanar da cewa mahajjata 60,000 ne kadai za a ba wa damar yin aikin Hajji a bana.
Hukumar Lafiyar Saudiyya, ta ce adadin mahajjatan zai hada da ‘yan asalin kasar da kuma baki masu shiga kasar.
- ’Yan bindiga sun sace mahaifi da dansa a Abuja
- Gobarar tankar mai ta jikkata mutum 64 a Kano
- A binciki mutuwar Janar Attahiru — Dalibai
Sanarwar ta ce “Mutane 60,000 ne kadai za su samu damar yin aikin hajji a bana, daga ciki da wajen Saudiyya.
“Wanda za su yi hajji dole su kasance daga shekaru 18-60, sannan ya zama wajibi su kasance cikin koshin lafiya.
“Dole maniyyata su gabatar da shaidar tabbatar da koshin lafiyarsu ta tsawon watanni shida, yayin zuwa aikin hajji,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta biyo bayan rashin tabbas da kasar ke ciki a kan aikin hajjin 2021, tun bayan barkewar annobar COVID-19 a 2020.
An rage adadin wanda za su yi aikin hajjin don bin matakan kariya daga cutar COVID-19, wanda kafin bullar cutar kasar na ba wa maniyyata miliyan biyu damar yin aikin hajjin.
Kazalika, sanarwa ta ce ya zama tilas ga duk wani maniyyaci ya gabatar da shaidar karbar rigakafin allurar COVID-19 kafin shiga kasar ta Saudiyya.