✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar matar Ganduje ta rasu

Mahaifiyar mai dakin Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa kuma tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ta rasu.

Mahaifiyar mai dakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa kuma tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ta rasu.

Da misalin karfe 2 na ranar Litinin din nan ake sa ran yi Hajiya Hasiya Muhammad Gauyama a Kano.

Za a yi jana’izar Hajiya Hasiya, mahaifiyar matar Ganduje, Farfesa Hafsat ne a gidan tsohon gwamnan da ke titin Miyango a Kano.

Mai magana da yawun shugaban na APC, Edwin Olofu ne ya sa and da rasuwar.

A wani salon ta’aziyya, Jam’iyyar ta mika jajanta ga iyalan Ganduje da ma ba marigayiyar tare da roka mata rahamar Allah.

Rasuwar ta so a daidai lokacin da ita ma mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa, Nana Shettima ta rasu a Kano.