✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar Gwamnan Oyo ta rasu

Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde rasuwa da safiyar Alhamis. Iyalan Misis Abigail Makinde, ta sakon da Barista Muyiwa Makinde ya…

Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde rasuwa da safiyar Alhamis.

Iyalan Misis Abigail Makinde, ta sakon da Barista Muyiwa Makinde ya fitar sun ce marigayiyar ta rasu ne tana da shekara 81.

“Mun gode wa Allah da Ya ba ta tsawon kana kuma za mu yi kewar ta saboda shawarwarinta da kuma shakuwa da ita musamman a tsakanin jikonkinta”.

Sanarwar wadda ta ce mahaifiyar gwamnan ta rasu ne ba tare da alamar rashin lafiya ba ta kuma yi godiya ga masu musu ta’aziyya.