Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda rasuwa tana da shekaru 93 a doron kasa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahaifiyar Gwamnan, Hajia Safara’u Umar Radda, ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Katsina.
Cikin wani saƙo da tsohon mai magana da yawun gwamnan, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Hajiya Safara’u ta riga mu gidan gaskiya bayan ta yi fama da doguwar jinya.
Sauran fitattun ’ya’yan Hajiya Safara’u sun haɗa da Dagacin Radda, Alhaji Kabir Umar Radda, da Hajiya Hauwa Umar Radda, tsohuwar matar marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’adua.
Wata sanarwa da Mataimakin Gwamnan Katsina, Malam Faruk Jobe ya fitar ta ce za a yi jana’izar Hajiya Safara’u da yammacin yau a garin Radda.
Rasuwar Hajiya Safara’u na zuwa ne a daidai lokacin da shi kuma Gwamnan Dikko Radda ya kasance yana kasa mai tsarki inda ya tafi Umara.
Mabiya dandalan sada zumunta na ci gaba da bayyana alhini dangane da rasuwar Hajiya Safara’u.