✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar Dahiru Mangal ta rasu

Mahaifiyar tasa mai suna Hajiya Murja Bara'u, ta rasu ne a cikin daren Juma'a tana da shekara 85.

Allah Ya yi wa mahaifiyar hamshakin dan kasuwa kuma Shugaban Kamfanin Jiragen Sama na Max Air, Alhaji Dahiru Mangal, rasuwa.

Mahaifiyar tasa mai suna Hajiya Murja Bara’u, ta rasu ne a cikin daren Juma’a tana da shekara 85 bayan gajeruwar rashin lafiya.

Dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina Mai wakiltar Katsina, Hon. Ali Abu Albaba, shi ne ya tabbatar da rasuwar a safiyar Juma’a ta shafinsa na Facebook.

Marigayiyar ta rasu ta bar ’ya’ya uku, maza biyu da mace daya, da suka hada da Alhaji Dahiru Mangal, Alhaji Bishir Bara’u da kuma Hajiya Zulai tare da jikoki da dama.

Kafin rasuwarta, Hajiya Murja ta zamo uwar marayu da almajirai ta hanyar ciyar da su da abinci a kullum.

Hatta da ’yan gudun hijirar da suke zaune a cikin garin Katsina a gidanta suke samun na karin kumallo.

Ana sa ran za a gudanar da Sallar Janai’zar mahaifiyar ta Dahiru Mangal ce bayan Sallar Juma’a a Masallacin Mangal da ke Kofar Kwaya, a garin Katsina.