✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar Dadiyata: Za a yi jana’izar bayan Sallar La’asar

Ta rasu bayn kimanin shekara uku da wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi awon gaba da shi a gidansa

Bayan Sallar La’asar za a yi Sallar Janai’zar mahaifiyar matashin malamin jami’ar nan da ya yi batar dabo, Abubakar Usman Idris, wato Dadiyata.

Usman Idris, wa ga Dadiyata ya ce za a sallaci mahaifiyarsu, Malama Fatima ne a gidansu da ke kan layin Gombe Road, garin Kaduna.

Malama Fatima ta rasu ne ranar Talata, 19 ga Afrilu, 2022, a Asibitin Sojoji na 44 da ke garin Kaduna, sakamakon rashin lafiya.

Wani abokin Usman na kut-da-kut, Lawal Muhammad, ya shaida wa Aminiya cewa da asubahi aka garzaya da ita zuwa asibitin, bayan wani lokaci kuma rai ya yi halinsa.

Rasuwar mahaifiyar Dayiyata na zuwa ne kimanin shekara uku da ake neman inda yake tun bayan da wasu da a san ko su wane ne ba suka je har gidansa da ke unguwar Barnawa a Kaduna suka tafi da shi da karfin tuwo.

Ba a sake jin duriyar Abubakar Dadiyata ba tun daga wannan lokaci, duk da kokarin da iyalan suka yi da gangamin neman ganin mahukunta sun gano inda yake, an kuma sako shi.

Abubakar Idris Usman malami ne a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin Ma a  Jihar Katsina.