✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahaifiyar Dadiyata ta rasu

Malama Fatima Abubakar ta rasu bayan fama da rashin lafiya a Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna.

Allah Ya yi wa Malama Fatima, mahafiyar matashin malamin jami’ar nan, Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, rasuwa a safiyar Talata.

Malama Fatima Abubakar ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya a Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna.

Wani makusancin iyalan na kut-da-kut, Lawal Muhammad, ya shaida wa Aminiya cewa da asubahi aka garzaya da ita zuwa asibitin, bayan jikin nata ya yi tsanani.

Malam Lawal, wanda amini ne ga wan Dadiyata, Usman Idris, ya tabbatar da cewa a halin yanzu, ’ya’yan marigayiyar na kan hanyarsu ta komawa Kaduna, bayan samun labarin rasuwarta.

A shekarar 2018 Abubakar Idris Dadiyata, ya yi batar dabo, tun bayan da wasu da ba san ko su wane ne ba suka yi awon gaba da shi a gidansa da ke Kaduna.

Tun daga lokacin ba a sake jin duriyar Abubakar Dadiyata ba, wanda malami ne a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin Ma da ke Jihar Katsina.

 

%d bloggers like this: