Ga dukkan alamu yarjejeniya ta kullu a tsakanin kulob din Manchester City da ke Ingila da matashin dan kwallo Kelechi Iheanacho bayan mahaifinsa da kuma kulob dinsa na da Taye Academy sun samu kason Fam dubu 300 kwatankwacin Naira miliyan 78 kowannensu.
A kwantaragin da dan kwallon ya yi kulob din Man City kafin dan kwallon ya sanya hannu sai an ba mahaifinsa da tsohon kulob dinsa kason Fam dubu 300 kowannensu, kuma tuni hakan ta tabbata.
Kafar sadarwar labarin wasanni ta Intanet MTNFootball.com ta kalato cewa tuni mahaifin dan kwallon da kuma kulob din Taye suka tabbatar mata da samun sako daga bankunansu a kan shigar kudin asusun ajiyarsu a karshen makon jiya.
“Mahaifin Iheanacho ya samu sako daga banki cewa kason da kulob din City ya ba shi na Naira miliyan 78 ya tabbata”, inji wata majiya da ke kusa da mahaifin dan kwallon.
A da kulob din Manchester City ya yanke shawarar sai a watan Janairun badi (2015) ne zai biya mahaifin da tsohon kulob dinsa wadannan kudi al’amarin da ya kusa rusa cinikayya a tsakaninsu amma ganin yadda kulob da dama a Nahiyar Turai suka yunkuro don dauke dan kwallon ta sa ala tilas kulob din canza shawarar kammala cinikin a wannan lokaci.
Yanzu dai Iheanacho ya fara neman takardar izinin shiga Ingila (Biza) ne don ba shi damar komawa kulob din City.
Sai dai rahotanni sun nuna kulob din City zai tura shi Ghana ne watau makatantar horar da matasan ’yan kwallon kulob din da ke can kafin ya samu kwarewar da za ta sa ya fara yin kwallo a matakin manya a kulob din a nan gaba.
Mahaifin Iheanacho ya samu Naira miliyan 78 a cinikin dansa
Ga dukkan alamu yarjejeniya ta kullu a tsakanin kulob din Manchester City da ke Ingila da matashin dan kwallo Kelechi Iheanacho bayan mahaifinsa da kuma …