Stanley Johnson, mahaifi ga Fira Ministan Burtaniya Boris Johnson, ya ce zai nemi izinin zama dan kasar Faransa don ci gaba da kulla kawance da kasashen Tarayyar Turai.
Stanley ya bayyana haka ne a yayin hirarsa da gidan rediyon RTL dake Faransa, inda ya ce kakarsa da mahaifiyarsa dukkaninsu ‘yan kasar ta Faransa ne.
- WHO ta fara tattaunawa da Birtaniya kan sabon nau’in COVID-19
- Gidan tarihin Birtaniya ya ba da $4m don gina gidan tarihi a Edo
“Ba wai iya batun zama Bafaranshe bane kawai, ina jin harshen kasar kuma ina da asali da su.
“Mahaifiyata da kakata dukkaninsu ‘yan asalin kasar Faransa ne. Don haka nima ina da ikon zama dan kasar,” inji Johnson.
A cewarsa shi ma yana da damar zama dan kasar Faransa, tunda yana da asali a can.
Stanley, mai shekara 80, a baya ya yi aiki a matsayin memba na Majalisar Tarayyar Turai (EU).
A ‘yan shekarun da suka gabata, iyalan Fira Ministan sun kasu kashi biyu dangane da batun ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai wato Brexit.
‘Yar uwarsa, Rachel, ta ci gaba da goyon bayan rusasshiyar jam’iyyar siyasa ta Canjin Birtaniya yayin da kuma dan uwansa, dan majalisa Jo, ya yi murabus daga mukaminsa saboda rikicin Brexit da ya barke a watan Satumbar bara.
Yayin taron jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya a watan Oktoba na 2019, Fira Ministan ya ayyana cewa mahaifiyarsa ta zabi ficewa daga EU.