✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifin dalibar da aka sace a kwalejin Kaduna ya rasu

Labarin garkuwa da ita ya sa jikinsa ya yi tsanani har ta kai ga mutuwa

Mahaifin daya daga cikin dalibai 39 da aka yi garkuwa da su a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Kaduna ya rasu.

Aminiya ta gano cewa an garzaya da dattijo Ibrahim Shamaki asibiti ne bayan labarin garkuwa da ’yar tasa ya sa rashin lafiyarsa ta tsananta.

“Tabbas ya rasu a Maradi, Jamhuriyar Nijar, idan Allah Ya yarda gobe (Asabar) za a dawo da gawarsa Najeriya. A makon jiya ne jikin nasa ya yi tsanani bayan samun labari cewa an yi garkuwa da ’yarsa,” inji surukin mamacin Abdullahi Usman.

An gano dalibar mai suna Fatima Ibrahim ne a bidiyon da ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su suka fitar bayan awanni da kai harin.

Wadanda suka san ta sun ce ita ce dalibar da aka gani sanye da lullubi a cikin bidiyon.

An yi garkuwa da daliban su 39 ne a tsakar dare daga kwalejin da ke Afaka a Kaduna, bayan dauki ba dadi tsakaninsu da jami’an tsaro mako biyu da suka gabata.

Sojoji sun kubutar da mutum 180 daga kwalejin zuwa barikin soji, sannan daga baya aka rufe makarantar.

Masu garkuwa da daliban 39 na neman kudin fansa Naira miliyan 500, amma Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi watsi da bukatar tasu da ma yiwuwar tattaunawa da su.