✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magoya bayan Super Eagles sun tara Naira miliyan 400 don tafiya gasar cin kofin duniya a Brazil

Shugaban kungiyar masu goyon bayan Super Eagles Rafiu Ladipo ya bayyana cewa kawo yanzu kungiyarsa ta tara kimanin Naira miliyan 400 a shirye-shiryen tafiyarsu gasar…

Shugaban kungiyar masu goyon bayan Super Eagles Rafiu Ladipo ya bayyana cewa kawo yanzu kungiyarsa ta tara kimanin Naira miliyan 400 a shirye-shiryen tafiyarsu gasar cin kofin duniya a Brazil a wata mai zuwa.
Sai dai ya ce kungiyar tana bukatar akalla Naira  miliyan 800 ne don tafiya gasar a Brazil.  Ya ce suna sa ran kungiyar za ta dauki dawainiyar membobinta su kimanin 800 ne don goya wa Super Eagles baya a Brazil.
“Ya zuwa yanzu za mu iya cewa mun tara kusan kashi 50 cikin 100 na kudin da muke bukata kuma muna sa ran samun sauran kashi 50 din kfin a fara gasar a wata mai zuwa a Brazil”, inji shi a lokacin da yake hira da manema labarai a Abuja.
A watan da ya gabata ne dai shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya tallafawa kungiyar da Naira miliyan 50 kuma shugaban ya yi alkawarin sanya wasu daga cikin mukarrabansa da kamfanoni masu zaman kansu su ma su ba kungiyar nasu tallafin kafin a fara gasar cin kofin duniya a Brazil.