Tsohon Mataimaki na Musamman ga tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, Reno Omokri ya ce magoya bayan Peter Obi na Kam’iyyar LP ba su isa su yi tattaki a mahaifar dan takarar ba.
Omokri ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce idan har maganganun da masoyan dan takarar shugaban kasar na Jam’iyyar ke fada cewa ya maida Jihar Anambra da ita ce mahaifarsa Aljannar Duniya, ina dalilin zamansu a Jihar Legas?
- Jami’ar Benin Ta Karyata batun janye yajin aiki
- Wane bangare ya fi samun kaso mai tsoka a kasafin 2023?
Ya ce idan suna son al’umma su dauki batunsa da muhimmanci, kamata ya yi su kwashe kayansu su koma mahaifar tasu.
Idan dai za a iya tunawa a ranar Litinin ne haramtacciyar kungiyar ’yan a-waren Biafra (IPOB) su ka sanya dokar zaman gida dole a duk fadin jihohin Kudu maso Gabashin kasar nan.
Omokri ya ci gaba da cewa, tsaro, da makarantu, da kiwon lafiya, da wutar lantarki da ake samu a Jihar Legas a halin yanzu sun fi na Jihar Anambra, kuma ma’aikatan gwamnati a Legas sun fi takwarorinsu na Anambra albashi mai kyau.
sai dai wani mai suna @OnwuofDelta, ya mayar masa da martani da cewa, “Obi na da kwararrun masana a masoyansa, kuma da zarar ya kammala shekaru 8 na gudanar da ingantaccen mulki a Najeriya, duk za su komawa sana’o’insu dabandaban da suke yi.
“Dalili dukkansu na da abin yi, ba jira suke su yi kashe mu raba ba da tattalin arzikin kasa, ya kamata dai a rage maganganu marasa amfani!”