✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magoya bayan Manchester United sun yi wa Alex Ferguson da David Moyes tofin Allah-tsine

Jim kadan da kammala a wasa a tsakanin kulob din Manchester United da na Manchester City da ke Ingila a gasar rukunin Premier na Ingila…

Jim kadan da kammala a wasa a tsakanin kulob din Manchester United da na Manchester City da ke Ingila a gasar rukunin Premier na Ingila a ranar Talatar da ta wuce ne magoya bayan kungiyar kwallon kafar United suka yi caa a kan tsohon Koci Sa Aled Ferguson da kuma Koci mai ci yanzu Dabid Moyes inda suka rika yi musu tofin Allah-tsine ganin yadda suka jefa kulob din cikin matsala a kakar wasa ta bana.
A wasan, City ce ta doke ta United da ci 3-0 da hakan ya sa kawo yanzu United ta yi rashin nasara a gasar sau goma, kuma shida daga ciki sun faru ne a filin wasanta na gida watau Old Trafford.
Da kyar da gumin goshi jami’an tsaro suka hana wasu daga cikin magoya bayan yaga wani hoton da ke makale na kocin Moyes a filin wasa na Old Trafford da aka yi wa ado da rubutun “Zababbe” ko The Choosen One” a Turance.
A bara ne dai Aled Ferguson ya yi ritaya inda ya zabi Dabid Moyes a matsayin sabon kocin United bayan ya shafe kimanin shekara 26 tare da lashe kofuna 13 a gasar Premier ta Ingila.
Haka su ma magoya bayan kulob din a sassan duniya ciki har da Najeriya sun nuna bacin ransu a kan yadda kulob din yake tangal-tangal a kakar wasa ta bana.