Wasu ’yan ga-ni-kashenin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid su biyu sun rasa rayukansu saboda bakin cikin ganin yadda kulob din ya kasa farke cin da kulob din Atletico Madrid ya yi masa a kan lokaci.
Wadanda suka mutn sun hada da Olusoga Ogunbanjo dan kimanin shekaru 39 wanda ke yin sana’ar gyaran firji da ke zaune a gida mai lamba 23 da ke kan titin Smith, sai kuma Bambo Sholeye, dan shekaru 42 da haihuwa, ma’aikacin hukumar tsaftace muhalli ta jihar, wanda ke zaune a gida mai lamba 49 da ke kan titin Apatire dukkansu a birnin Ikko.
Rahotanni sun nuna cewa Sholeye ya je kallon wasan ne a wani shago daga bisani sai ya fito cikin fushi kafin a kare wasan yana ta bayyana bakin cikinsa da kulob din Real Madrid da ya kasa farke kwallon da Atletico ya jefa masa a farkon rabin lokaci.
Rahotannin sun ce ya zauna a kofar gidansa yana ta bayyana bakin cikinsa, sai kawai ya yanke jiki ya fadi inda nan take ya mutu duk da kokarin da likitoci suka yi na farfado da shi yayin da aka kai shi asibiti.
Shi kuwa Ogunbanjo an ce ya je shagon aski ne don a yi masa aski daga nan sai yanke shawarar kallon kwallon da ake yi da kulob dinsa Real Madrid da Atletico Madrid. An ce yayin da kulob dinsa Real Madrid suka kasa farke kwallon dayan da Atletico ya ci su sai kawai ya yanke jiki ya fadi. Bayan an kai shi asibitin gwamnatin Jihar Legas sai likitoci suka bayyana cewa ya mutu.
Wata majiya ta bayyana cewa wani yaro da ke kusa da shi ne ya sanar da masu kallon wasan cewa Ogunbanjo ya fadi kasa.
Sai dai kulob din Real Madrid daga bisani ya farke cin da Atletico Madrid ta yi masa inda aka tashi ci wasa ci 4-1 da hakan ya sanya Madrid lashe kofin a karo na 10 a tarihin gasar.
Sai dai rundunar ’yan sandan jihar Legas ta bayyana cewa lamarin bai kai gare ta ba a lokacin da aka tuntube ta.
Magoya bayan Madrid biyu sun mutu a Legas
Wasu ’yan ga-ni-kashenin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid su biyu sun rasa rayukansu saboda bakin cikin ganin yadda kulob din ya kasa farke cin…