Jim kadan da kammala wasa a tsakanin kulob din Liberpool da na Chelsea da ke Ingila a gasar rukunin Premier ne magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar biyu suka ba hammata iska.
Kulob din Chelsea ne ya yi tattaki har filin wasa na Anfield da ke Liberpool inda ya lallasa Liberpool da ci 2-0 da hakan ta jefa kulob din cikin mayuwacin hali a yunkurin da kulob din yake yi na lashe gasar rukunin Premier a bana.
Kafin wasan, Liberpool ne ke saman tebur da tazarar maki biyar a kan kulob din Chelsea amma lallasawar da Chelsea ta yi wa Liberpool yanzu tazarar ta koma biyu ne kacal a tsakaninsu kulob yayin da kulob din Manchester City yake biye da tazarar maki uku. Kenan idan City ta samu nasara a kwanton wasanta za ta haye saman tebur a gasar.
Magoya bayan Liberpool ne suka fara takalar na Chelsea don hushe haushin cin da aka yi musu amma na Chelsea suka tanka kuma nan take suka rika ba hammata iska. Da kyar jami’an tsaro suka shiga tsakani kuma sun kama da yawa daga cikin wadanda suka yi fadan inda suka tasa keyasrsu zuwa ofishinsu don ci gaba da gudanar da bincike.
kwallaye biyun da ’yan kwallon Chelsea Demba Ba da Willian suka jefa a ragar Liberpool ne suka ba Chelsea damar samun nasara a wasan.
Yanzu dai ya rage saura wasanni biyu a kammala gasar kuma akwai yiwuwra kungiyoyin kwallon kafa uku watau na Liberppol da na Chelsea da kuma na Manchester City ne ake sa ran daya daga ciki zai zama zakara a gasar ganin yadda suke bin juna gab da gab.
Magoya bayan Liberpool da na Chelsea sun dambace
Jim kadan da kammala wasa a tsakanin kulob din Liberpool da na Chelsea da ke Ingila a gasar rukunin Premier ne magoya bayan kungiyoyin kwallon…