✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Magoya bayan APC da PDP sun ba hammata iska a Filato

Mutane da dama sun jikkata sakamakon arangamar da magoya bayan jam'iyyun suka yi.

Magoya bayan jam’iyyun APC da PDP sun yi arangama a yankin Sabon Gida da ke Karamar Hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato.

Binciken Aminiya ya gano lamarin ya faru a ranar Asabar lokacin da ake tsaka da bikin samar wa da ’yan kabilar Tarok matsuguni a Jihar.

Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa, Lanchang Timpil, ya ce fadan da ya rikide ya koma na siyasa a tsakanin matasan yankin, a lokacin da Ubandoma Laven ya halarci taron.

Sai dai bayaninsa a wajen taron bai yi wa Honarabul Vincent Bulus Venman, wanda shi ne sabon shugaban Langtang, dadi ba.

Lamarin ya yi sanadin tada tarzoma a tsakanin magoya bayan bangarorin biyu, wanda suka fito daga APC da PDP, wanda hakan ya jikkata mutane da dama.

Kakakin ’yan sandan Jihar, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kuma ce tuni rundunarsu ta fara gudanar da bincike don gano hakikanin abin da ya haddasa tarzomar.