Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Bisa la’akari da wannan wata mai albarka da muke ciki, za mu gabatar da tunatarwa ga magidanta kan kulawa da amanar da Allah Ya dora musu game da iyalansu. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Umarnin Allah Ga Magidanta: Allah SWT Ya dora muku babban nauyi, inda Ya umarci ku kare kanku da iyalinku daga wata wuta, wacce makamashinta suka kasance mutane da duwatsu, (kur’an: Sura ta 66, Aya ta 6). Sai dai abin takaici kadan ne daga cikin magidantan wannan zamanin ke kokarin aiki da wannan umarni na Allah SWT, yayin da mafi yawansu ke sakacin kyale iyalinsu, suna ketare iyakokin addini a kan idonsu da sanin su ba tare da sun taka musu burki ba.
Wasu kuma sukan shagala da ayyukan neman duniya har ba su san halin da tarbiyyar iyalinsu ke ciki ba. Don haka wannan wata na Ramadan babbar dama ce ga irin wadannan magidanta, don su binciki kansu tun kafin ranar nadama ta zo. Su sani cewa, kula da tarbiyyar iyalinsu da tabbatar da cewa ba su ketare iyakokin addini ba, shi ne mafi girman soyayyar da za su ba iyalinsu; wanda a dalilin haka za su more a duniya da kuma a lahira suna masu rabauta da Aljannar ni’ima cikin yardar Allah SWT; kuma yin haka shi zai sa su zama masu mutunci a idon duniya da kuma a lahira, Allah Ba zai zarge su game da iyalinku ba.
Ga wasu hanyoyi da magidanta za su yi amfani da su a cikin wannan wata mai albarka da kuma bayansa don su aza iyalinsa a kan hanyar alheri da za ta tserar da su daga wuta cikin yardar Allah:
1. Zama Malami Ga Iyalinka: Wata kyakkyawar hanya da maigida zai bi wajen samar wa kansa da iyalinsa dacewa da dukkan alheran da ke cikin Ramadan shi ne, sai ya rikide ya zama malami ga iyalinsa; yin haka abu ne da maigida da iyalinsa za su amfana, kuma su nishadantu da shi. Sai a fitar da wasu ranakun da suka dace, kamar sau uku a mako, sannan a kebance wasu awowi a ranakun inda maigida zai zauna tare da iyalinsa, sannan ya rika koyar da su abubuwan ilmi.
Maigida zai yi nazarin irin ilmin da zai amfani iyalinsa, ya kuma habaka tarbiyyarsu. Idan ya kasance maigida ba shi da isasshen ilmi a fannin da yake son karantar da iyalinsa a kai, to sai ya yi bincike, ya zauna, ya tsara laccarsa kafin gabatar da ita ga iyalinsa.
Misali, maigida na iya koyar da iyalinsa hukunce-hukunce da muhimmancin wannan wata na Ramadan da tarihin Annabawa da tarihin Sahabban Manzon Allah SAW da tarihin yake-yaken Musulunci da sauransu.
Kowane bangare da maigida ya dauka, to sai ya dage wajen gabatar da shi ta siga mai kyawu, ana yi ana raha, ta yadda dalibansa za su fahimta sosai, kuma su amfana da darasin da ke ciki. Misali, idan tarihin Sahabban Manzon Allah SAW ya dauka, sai ya yi kokarin bayyanar da tsarkin zuciyarsu da kyawun halayyarsu da karfin imaninsu da jaruntakarsu da sadaukarwarsu, don daukaka Musulunci da kuma tsarkakakkiyar soyayyar da suke yi wa Manzon Allah SAW. Kuma duk maudu’in da maigida ya gabatar, sai ya yi sharhi kan darussan da ke cikinsa don karin fahimta, sannan ya kwadaitar da su dagewa wajen yin koyi da darussan da ke ciki, don a samu dacewa da alherin duniya da lahira.
A karshen kowane darasi, sai a ba kowa damar yin tambaya ko neman karin bayani. Bayan kammala gabatar da maudu’in gaba dayansa, maigida na iya yin jarrabawa ga dalibansa, tare da bayar da kyauta ga wadanda suka yi zarra a jarrabawar.
Wannan abin dadi da nishadantarwa ne da ya kamata a adana, don haka idan da hali sai a dauka a bidiyo a adana don gaba. Kuma wani abin alheri ne da ya kamata maigida ya ci gaba da shi har bayan azumi, ba wai sai cikin azumi kawai ba.
2. Zama Sabon Ango Ga Uwargida: Babbar sifar da aka san kowane sabon ango da ita, ita ce: cike yake da tsananin soyayyar matarsa da ji da ita, zuciyarsa cike take da shau’ukan soyayyarsa gare ta; kallon da idanuwansa ke mata, kallon kauna da darajawa ne; yana son jiyar da ita dadi da nuna mata bajintarsa gare ta; yana yin komai take so, ko ta nema daga gare shi, zai biya mata bukatarta. To haka ya kamata kowane maigida ya kasance ga matarsa cikin wannan wata mai albarka.
Sannan ya kara da saukaka mu’amalarsa da ita, ta hanyar yin hakuri da kau da kai ga kura-kurenta da nakasun da ya bayyana a halayyarta, ko mu’amalarta da shi. Maigida ya sani cewa aure babbar ibada ce, wacce in ya kyautata ta cikin wannan wata mai alfarma, za a nunnunka masa lada; don haka duk lokacin da ka yi wa matarka kallon kauna da darajatawa, tare da lallausan murmushi, to lada za ka samu, musamman in ka yi da niyyar kyautata ibadar auratayya ne.
Saboda haka a daure, a tausasa zuciya, a kuma kara kyautata wa uwargida a cikin wannan wata, ta hanyar rage mata ayyukan gida, misali, kamar da safe kafin fita aiki, sai maigida ya duba ayyukan gida da suka fi nauyi ya rage wa uwargida: kamar yi wa yara wanka da shirya su, share gidan gaba daya, zubar da shara da duk wani abu da ka san in ka dauke mata nauyin a wannan rana za ta ji saukin sauran ayyukan.
Magidanta: Ku bi Umarnin Allah Game Da Iyalinku
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Bisa la’akari da wannan wata mai albarka da muke ciki, za mu…