Wani dattijo mai shekaru 60 ya gurfana gaban kotu saboda barazana ga rayuwar matarsa da kuma kurarin yada hotunan tsiriacinta.
Muutm ya shiga hannu ne bayan ya tuttura wa matar tasa sakonnin barazaar ta wayanta, bayan wani sabani da ma’auratan suka samu.
- An cafke ‘yan Kano masu sayar da hotunan mata na batsa
- Harin Boko Haram kan turakun lantarki ya jefa Maiduguri cikin duhu
- Kotu ta raba auren shekaru 12 saboda saurin fushin mata
- Ya gurfanar da matarsa a gaban kotu bisa zargin yunkurin kashe shi
Bayan gudanar da bincike ne ’yan sanda suka cafke magidancin, suka gurfanar da shi a gaban Kotun Majistare da ke zamanta a Ikeja, bisa zarginsa da tada hankalin matar da kuma neman ta da zaune tsaye.
Mai gabatar da kara, ASP Kehinde Ajayi, ya shaida wa kotu cewa mutumin ya aikata laifin ne a ranar 11 ga Disamba, 2020, a Ikeja.
Ya ce laifukan sun saba da Sashe na 168 da 56 na Dokar Manyan Laifuka ta Jihar Legas ta 2015, wanda ya tanadi daurin shekara daya a gidan yari, ga wanda ya aikata laifi irin wannan.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata lafin da ake zargin sa da aikatawa.
Alkalin kotun, Misis A.O Ajibade, ta bayar da belin wanda ake karar a kan kudi N100, 000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
Ta kuma dage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu, 2021.