✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Magidanci ya kashe uwar ‘ya’yansa, ya kuma kashe kansa

Rundunar ‘Yan Sandan Farin Kaya masu Bincikar Manyan Laifuka ta SCIID da ke Panti a Yaba, Jihar Legas na bincike a kan zargin wani mutum…

Rundunar ‘Yan Sandan Farin Kaya masu Bincikar Manyan Laifuka ta SCIID da ke Panti a Yaba, Jihar Legas na bincike a kan zargin wani mutum da kashe farkarsa ya kuma kashe kansa.

Ana zargin mutumin mai shekaru 39 dan rukunin gidaje na Victory Point a Legas, ya kashe Olamide Alli wadda suka yi zaman daduro da ita, ta haifa masa ‘ya’ya biyu. Hakazalika ana tuhumar mamacin da kashe kansa bayan ya kashe matar.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an gano gawar matar na a kwance cikin jini da kuma mummunan sara a kanta, yayin da shi mutumin aka ga gawarsa da alamar kumfa da ke fita daga bakinsa, lamarin da yasa ake zargin guba ya sha ya kashe kansa.

Kakakin ‘yan sanda na Legas DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Lahadi 21 ga watan Yuni rundunar ta sami rahoto cewa an gano gawar mutanen a gidansu.

Ya kara da cewa jami’an rundunar sun killace wajen da lamarin ya faru domin gudanar da bincike, “Ana zargin mutumin ya hallaka matar ne da wuka, sannan ya sha guba ya kashe kansa.

“An gano wukar kicin guda biyu da jini a jikinsu, da kuma robar maganin kashe kwari guda biyu da gwangwanin lemon kwalba mai kara kuzari wadanda duka an yi amfani da su a wajen da aka yi kisan”, inji shi.

Bala Elkana ya kara da cewa ‘yan uwansu sun ce, “mutumin da matar sun dade suna zaman daduro na tsawon shekaru 7 kuma a hakan suka haifi ‘ya’ya biyu maza biyu, masu shekaru bakwai da uku.

“Daga baya zaman nasu ya ki dadi ta yadda suka raba gari, a lokacin da mijin ke zaune a yankin Ilasan, matar na zaune ne a unguwar Ogba” inji shi.

Bala Elkana ya ce  matar ta ziyarci uban ‘ya’yanta cikin dare kwana guda kafin faruwar lamarin, “mutumin ne ya bukaci ta zo wajenshi, da zata je sai ta nemi kanwarta mai shekaru 22 ta yi mata rakiya.

“Kanwarta ce ta fara gano gawarsu, a jawabin da ta rubuta mana, ta ce karar kida da aka kunna a dakin mamatan ne ya tsahe ta daga barci, domin ita da yaran sun kwanta ne a wani dakin daban da na mamatan”, inji shi.

Ya kara da cewa zuwa yanzu ba a gano dalilin da ya sa mutumin ya aikata haka ba, amma ana ci gaba da bincike.