Wani magidanci ya caccaka wa matarsa da ke dauke da juna biyu wuka a Babbar Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano.
Magidancin ya zaro wuka ya rika caccaka wa matar da wanta ne bayan zaman kotun da ta kai kara kuma alkali ya raba aurenta da tsohon mijin nata.
- Kiris ya rage Obasanjo ya yi min ritaya shekaru 21 da suka wuce —Buratai
- Karin ’yan matan Chibok sun tsere daga hannun Boko Haram
- Bidiyon Dala: Kotu ta fitar da ranar ci gaba da shari’ar Ganduje
- PDP ta bukaci Kotun ICC ta hukunta tsoffin Hafsoshin Tsaro
Matar ta ce ta nemi kotun Musuluncin da ke zamanta a Karamar Hukumar Rano da ta raba aurenta da tsohon mijin nata ne saboda yana hana ta abinci, yana kuma cutar da ita.
Matar mai suna Shafa’atu Sale ta ce, “Alkali ya ce in ba shi sadakinsa N20,000 amma ya ki karba, sai ya karba a hannun [dan uwana] Ado.
“Da muka fito daga kotu shi ne ya dinga bin mu, sannan ya zaro wuka ya fara caka wa Ado a ciki ni ma ya rika caka min.”
Da yake kwatanta abin da ya faru, wan matar mai suna Ado ya ce da kyar ’yan sanda suka kwace shi da kanwarsa a hannun tsohon mijin nata.
Ya ce tsohon mijin kanwar tasa “ya biyo mu ta baya ya caka min wuka a cikina da sauran sassan jikina.
“Da kyar na ruga da gudu zuwa bakin kotu; ban yi zaton zai caka mata wukar ba.
“Shi ne ’yan sanda suka zo su ma da kyar suka kama shi, sai da suka harba bindiga.”
Kano Focus ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin.