✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maganin gargajiya ya kashe yara ya kwantar da mahaifiyarsu a Kano

Binciken ya gano cewa shan maganin gargajiyar ne ya yi ajalin yaran.

Wasu kananan yara biyu, Maryam Abubakar da Abdulkadir Abubakar sun rasu sakamakon shan maganin gargajiya.

Mahaifiyar yaran kuma na asibiti ranga-ranga tana amsar magani bayan shan maganin da ta yi.

Wakilinmu ya rawaito cewar, lamarin ya faru ne a unguwar Kwarin Barke da ke Sabuwar Gandu, Karamar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano a ranar Talata.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan Jihar Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce an gano kwalbar maganin gargajiyar da suka sha a kusa da gawar yaran biyua.

Ya kara da cewa an gona maganin gargajiyar ne ya yi sanadin ajalin yaran tare da jinyatar da mahaifiyarsu.

Tuni ’yan sanda suka dauke gawarwakin zuwa Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa, inda aka tabbatar da rasuwarsu.

’Yan sandan ta fara gudanar da bincike kan lamarin.