A daidai lokacin da yanayin sanyi ke kunno kai, an gargadi ’yan Najeriya su daina taruwa a cikin daki daya sannan su kasance cikin lura saboda yiwuwar barkewar cutar sankarau. Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa Kasa [NCDC] ce ta yi wannan gargadi bayan da lokacin annobar ya fara karatowa, wanda yakan fara ne daga watan Nuwamba, sannan ya yi kamari a tsakankanin Afrilu, kuma ya tsaya a watan Yuni.
Najeriya na daya daga cikin kasashen Afirka da suke fama da annobar sankarau, inda ake samun barkewar annobar duk shekara a akalla jihohi 26, wadanda suka hada da Babban Birnin Tarayya da jihohin Zamfara da Katsina da Sakkwato da Kebbi da Neja da Adamawa da Yobe da Gombe da Nasarawa da Borno da Kuros Ribas da Jigawa da Kaduna da Kano da Legas da Filato da Osun.
Domin magance aukuwar lamarin kamar yadda ya wakana a shekarar 2016 zuwa 2017, Cibiyar NCDC a rahotonta na mako-mako, ta yi kira ga dukan jihohin kasar nan 36 da Babban Birnin Tarayya su kara kaimi wajen shiri da bincike, domin cutar za ta iya yaduwa daga jihohi 26 da aka saba, zuwa wasu sassan kasar nan. Cutar sankarau cuta ce da ake dauka ta hanyar haduwa da mai ita. Idan an samu alamar cutar,Cibiyar NCDC ta shawarci jihohi da su gaggauta yin gwaji a dakunan gwaji na jihohinsu.
Olawu Aderinola, wanda shi ne jagoran Kwamitin Yaki da Sankarau na Cibiyar NCDC, ya ce cutar muguwar cuta ce, “Idan ba a magance ta ba, za ta iya kashe zuwa kashi 50 na wadanda suka harbu da ita,” inji shi. Ya kuma kara da cewa, “Matsalar cutar ita ce duk da cewa ana magance ta idan an gano ta da sauri, kashi 10 zuwa 20 na wadanda suka tsira, za su iya kamuwa da wata cutar ta nakasa. Idan aka dade da sankarau kuwa takan jawo manyan cututtuka kamar zama kurma da kuturta da sauransu. Don haka ne Aderinola ya shawarci ’yan Najeriya su rika gaggauta zuwa asibiti idan suka fara jin zazzabi.
Cutar sankarau cuta ce da ke kumbura marufin kashin baya da kwakwalwa. A Najeriya, akwai nau’o’in sankarau da daban-daban da suka hada nau’in A da B da C da W da D da Y. Manyan alamun cutar sun hada zazzabi da ciwon kai da kagewar wuya. Sauran sun hada da amai da rashin son ganin haske da sauti da sumewa. Duk da cewa kwayar cutar sananniya ce, kadan daga ciki ne ake iya kiyaye aukuwarsu ta hanyar rigakafi. Sankarau cuta ce da ka iya hallaka mutum saboda kusancin kumburin da take jawowa da kwakwalwa da kashin baya. Wannan ne ya sa ake alakanta cutar da mai neman agajin gaggawa.
Ya kamata gwamnatoci a matakan jihohi da kananan hukomomi su fara wayar da kan mutane a kan abin da ke jawo cutar da kuma alamominta. Ya kamata a ilimantar da al’umma a alfanun kwanciya a dakin da iska ke gudana da rage cunkoso a waje daya musamman a cikin dare. Masana a kiwon lafiyar al’umma sun nuna cewa tsabta tana daga cikin manyan hanyoyin kariya daga sankarau musamman a wuraren da mutane suke da yawa kamar sansanonin ’yan gudun hijira da gidajen yari da makarantu da asibitoci. Ya kamata a fara ilimantar da al’umma ne a irin wadannan wurare.
Kuma yana da muhimmanci gwamnatocin jihohi da kananan hukomomi su bayar da cikakken bayani a kan cibiyoyin maganin cutar. A matsayin cutar mai bukatar agajin gaggawa, ya kamata a samar da kayayyakin aiki a dakunan gwaji. A cikin shirinta na fuskantar sankarau, ya kamata gwamnati a dukan matakai ta tsara bayar da agajin gaggawa wanda zai hada da samar da isassun magunguna a cibiyoyinsu. Idan kuma aka samu barkewar cutar a jihohin da aka saba, to ya kamata a yi duk mai yiwuwa wajen kare yaduwarta ta hanyar nemo rigakafin cutar daga cibiyoyin duniya.
Ya kamata Ma’aikatar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya ta hada hannu da sauran ma’aikatu da suka hada da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko [NPHCDA] da Cibiyar NCDC domin ganin an yi shirin da ya kamata a jihohin da suka saba da annobar sankarau domin rage aukuwa da yaduwar cutar.