An wayi garin ranar Asabar, 9 ga watan Oktoba, 2021, da labarin rasuwar mashahuriyar mawakiyar Hausa, Magiya Dambatta, wadda sunanta na asali Halima Malam Lasan.
Kafin rasuwar Magajiya Dambatta bayan gajeruwar rashin lafiya, tana da shekara 86, mun yi wata hira da ita, kuma hirar ta tattaro kusan duk abin da kuke son sani game da mashahuwariyar mawakiyar.
Halima, wadda ta fara waka tun tana ’yar budurwa, ta kuma yi tashe matuka a shekarun 1970 zuwa 1980 ta ce, “Tun ina da shekara 12 da haihuwa na fara waka. Ina zuwa wasa wurare daban-dabn, ba ma a cikin garinmu kadai ba, har ma da gefen garinmu da suka hada da Sharon Dunawa da Sharon Gulbi.
“A wancan lokacin idan na je fili idan ba ni na yi waka ba to taron ba ya dadi. Idan na je wuri ba zan yi waka ba to zan kwace makadin na gudu,” inji ta a hirar da muka yi ita.
Masana da masu sharhin wakokin Hausa na dauri sun yaba da wakokinta da irin tasirin da suka yi a rayuwar Hausa.
Masu sharhi na alakanta yawaitar sanya yara a makarantun boko a shekarun 1980 da irin tasirin wakar Halima Malam Lasan – Magajiya Dambatta.
Baya ga irin tashe da shahara da ta yi, ta kasance cikin manyan mawaka da duniyar Hausa ke tunkaho da su a wancan lokaci.
Baya ga wancan tasiri da rayuwarta ta yi a shekarun baya, daga baya sai aka nemi Malama Halima, aka rasa, bayan da ta samu lalurar makanta; Wadanda suka san ta kuma suka manta da ita, matasa kuma da ma can ba su santa ba.
Daga farkon rayuwarta zuwa lokacin da ta samu lalurar makanta har zuwa lokacin da ta koma ga Mahaliccinta kuma, rayuwarta ta kasance mai cike da darasi mai yawa.
Hirar karshe da Magajiye Dambatta
A tattaunwar da Aminiya ta yi ta karshe da zabiyar, wadda ta fara waka ce tun tana da shekara 12, ta ce mana ta yi karatun addini tun tana da kuruciyarta, daga baya ne ta tsunduma harkar waka gadangadan.
Ta yi wakoki da dama, kuma ta shahara a shekarun 1980 ta yadda idan ba ta je taro ta yi waka ba, taron bai cika yin armashi ba.
Ta ce sun hadu da Shata a lokacin bikin cikar Gidan Rediyon Najeriya Kaduna shekara 30, inda ta rera wakarta mai suna ‘Soriyal’.
Daga cikin wakokinta da ta tuno da su a lokacin hirarmu da ita, “Akwai wakar Soriyal da Wakar Taron Gidan Rediyon Kaduna da Wakar A Kama Aikin Gona da Wakar A sa yara makaranta da Wakar Jihar Jigawa da sauransu… Shekarun da yawa.
“Lokacin ina kan hanyata ta dawowa daga Minna inda Makaman Nupe ya gayyace mu biki sai aka fada min cewa za a yi wasa na bikin cikar gidan Rediyon Kaduna shekara 37.
“Da muka je dukkanin mawaka sun taru su Alhaji Mamman Shata Katsina da sauransu, sai aka nemi na yi waka, nan ne na hau na yi wakar nan tawa ta ‘Soriyal’ wacce kuma daga baya ta shahara.”
Ma’anar Soriyal
A wani faifan bidiyo da Jaafar Jaafar ya saka, an tambaye ta ma’anar Soriyal da ta ambata a wakarta, sai ta ce, “Daurin kallabin da nake yi. Ka san lokacin gyauto nake daurawa, sannan ga jakata, sannan ga mai barewa. Lokacin mai barewa.” Har ta ce ko za a dauko mata gyauton kallabi ta yi daurin.
Yadda ta makance
A lokacin hirar tamu da ita ta ce, “Yau kimanin shekara 11 ke nan da na makance gaba daya. [Amma] Dama tun ina da shekara biyu da aure idona daya ya sami hakiya.
“A lokacin ina Fagge har aiki an taba yi min amma idon bai samu ba. Daga baya sai kuma dayan idon shi ma ya kamu da ciwo.”
A hirar tamu da ita, ta ce, a lokacin ’ya’yanta biyu maza, sai kuma jikoki 10.
Begen mawakiyar
Bayan dogon lokaci tana tashe, sai kwatsam ta yi batar dabo, inda aka daina jin duriyarta, har ana iya cewa wadanda suka san ta sun fara mantawa da ita, matasa kuma da ma can ba su santa ba.
Bayan dogon lokaci, sai kwatsam a ranar 23 ga Disamban 2020, dan Editan jaridar intanet ta Daily Nigerian, Jafar Jafar, ya yada wani bidiyon Magajiya Dambatta na wakar ‘Soriyal’ da ta yi a Gidan Rediyon Najeriya Kaduna na bikin cika shekara 30.
A kasan bidiyo da Jaafar Jaafar ya dora a shafinsa na Facebook, sai ya rubuta da Ingilishi cewa, “Ku nishadantu da zakin muryar zabiya Magajiya Dambatta. Ina fata za ku ji dadin karshen mako.”
Cikin dan kankanin lokaci bidiyon ya karade gari, inda aka tura wakar sau kimanin 1,000, baya ga daruruwan tsokaci da aka yi a kai, bayan wadanda suka nuna alamar motsin rai domin nuna yadda abin ya burge su.
Masu tsokaci a kan bidiyon na Magajiya Dambatta sun suka rika tuna lokacin da take tashe, wasu kuma suna tuno lokacin da Gidan Rediyon Najeriya na Kaduna ke yawan sanya wakarta.
Daga cikin wadanda bidiyon ya burge su, wadansu sun san ta, wadansu sun ji labarinta, wadansu sun ji wakarta, wadansu kuma lokacin suka san ta.
Dawowar Malama Halima
A lokacin, daga cikinsu masu tsokaci kan bidiyon da Jaafar Jaafar ya dora akwai wani, Munzaili Hausawa, wanda baya ga sanin ta da ya yi, yana da labarin inda take – wanda ya yi silar gano ta.
A ranar 23 ga watan Disamban, Jaafar Jaafar ya sake wallafawa a shafinsa na Facebook cewa, “Na hadu da Magajiya Dambatta mai shekara 84 a gidanta da ke Makoda a Jihar Kano.
“Bayan na wallafa tsohon bidiyonta, wani abokina da ke aiki a Gidan Rediyon Kano, Munzali Hausawa, ya sanar da ni cewa tana raye.
“Wannan ya sa na tuka mota na tsawon kilomita 70 domin ganin ta cikin tsufa.
“Magajiya wadda yanzu makauniya ce ta bayyana mini yadda take rayuwa da abin da ta samu ta hanyar bara a kauye.
“Zakin muryarta yanzu ya fara dushewa, amma ta rera min wasu daga cikin fitattun wakokinta.
“Babban makadinta da mai biye masa, (Dan Kuntukuru) duk sun rasu, amma yawancin masu amshi wadanda a lokacin matasa ne suna raye,” inji shi.
Jafar Jafar ya kara da cewa, “Kamar yadda wani rubutu da aka yi game da wakokinta, wanda tsohon Manajan Daraktan Gidan Rediyo Kano, Adamu Salihu ya rubuta, wata wakar wayar da kan mutane a kan muhimmancin sanya yara a makaranta da ta yi a shekarun 1970 ta taimaka wajen sanya yara sama da 3,000 a makaranta.
“Ina tsammanin daga cikin yaran da a lokacin iyayensu suka sanya a makarantar a wancan lokacin yanzu wadansu sun zama farfesoshi.
“Amma ita Magajiya tana rayuwa cikin talauci mai tsanani. A Najeriya haka mutum ke yin tashe, sannan ya fado kasa kamar ba a yi shi ba,” inji shi.
Yadda aka tara mata N5m
Bayan Jaafar Jaafar ya wallafa wannan rubutu na biyu, rubutun ya yi yawo matuka, inda kusan mutum 1,100 suka yi martani a kansa, sannan 2,800 suka yada shi.
Daga cikin masu sharhi ne suka rika cewa ya kamata a tallafa mata, wadansu ma har suka fara daukar alkawarin bayar da gudunmawa.
Daga cikinsu, Dokta Ibrahim Musa ya ba da shawarar cewa za a iya tara Naira miliyan domin tallafa mata.
Bayan nan ne Jaafar Jaafar ya sake cewa ana ta kiran sa a waya cewa ya kamata a tallafa mata ta hanyar tara mata kudi.
Ya ce, “Fitaccen ma’aikacin taimako da ya kwashe sama da shekara 20 a harkokin jinkai, Musa Abdullahi Sufi, ya ce zai bayar da asusun ajiyar wata gidauniyar da yake cikin Kwamitin Amintattunta, sannan zai rika ba Dokta Ibrahim Musa da ni (Jaafar Jaafar) bayanai kan yadda ake ciki na tallafin da ake samu.
“Ni kuma zan rika bayyana wa mutane yadda ake ciki. Burinmu shi ne mu sake gina mata gida, mu saya mata kayan sawa da abinci. Bari mu ga yadda abin zai kasance.” Sai ya sanya asusun ajiyar da za a rika tura kudin.
Cikin kwana uku aka tara kudin da aka yi mamaki, inda a ranar farko mutum 43 suka tara Naira dubu 402 da 300.
Zuwa rana ta uku, mutum 367 sun tara Naira miliyan 2 da dubu 921 da 100, kamar yadda Ibrahim Sanyi-Sanyi ya wallafa a shafinsa.
An kyautata mata rayuwarta
A karshe Jaafar Jaafar ya ce an tara Naira miliyan 5 da dubu 6 da 222, sannan ya ce sun je gidan tsohuwar mawakiyar, sun tattauna da ’yan uwanta da makwabta da dattawan gari kan yadda za su tallafi rayuwarta.
Ya ce, “Bayan mun je gidanta ni da Musa Abdullahi Sufi da Ibrahim Sanyi-Sanyi da Munzali Hausawa, mun bayyana mata nasarar da aka samu wajen tara kudi.
“Ta yi godiya gare mu da kuma wadanda suka tara kudin. Sannan ta tabbatar mana cewa ta daina bara.
“Tuni Dokta Kabir Abdussalam ya duba idonta. Za a kai ta Asibitin Koyarwa na Aminu Kano domin duba lafiyarta. Muna fata idonta zai bude bayan an yi mata tiyata.
“Tuni mun sanya ejan ya nemo mana gida ko fili a kauyen da za mu gina mata gida ko mu saya. Wasu daga cikin kudin da aka tara za mu yi amfani da su wajen saya ko gina mata gida,” inji shi.
Daukar nauyin kula da ita
An kuma tsara yadda za a rika kula a ita na tsawon shekara uku, inda a duk shekara za a ba ta Naira dubu dari biyar sittin.
Kudaden da zaka ware mata sun hada da kudin kashewa da na sabulu da man shafawa da turare, sai kudin kayan salla, da na kula da lafiyarta, da kudin da abinci da mai da sabulu da kuma kula da lafiya har da na abinci.
Akasarin kudin ana ba ta ne kai tsaye, in banda kudin abincinta da za a bayar ta hannun jikanta mai kula da ita, sai kudin kashewa da za a ba wa ’yar jagorarta ta hannun mahaifiyarta.
Tsarin biyan kudaden
Za a ba ta kudin kashewa na tsawon shekara uku inda za a rika ba ta N5,000 kai-tsaye a duk kwana 10.
Duk kowane wata uku za a ba ta N15,000 na sabulu da man shafawa da turare — N5,000 ke nan duk wata.
Sai kuma N5,000 a duk wata na kula da lafiyarta.
Kowane bikin sallah za a ba ta N20,000 na kayan Sallah, wanda za a ba ta kafin sallar.
Kudin abincinta N12,000 duk wata wanda za a rika ba jikanta da ke ciyar da ita. N144,000 ke nan a shekara.
’Yar jagorarta kuma za a biya ta N3,000 kudin kashewa a makaranta duk wata, wato N100 kullum. Za a rika ba mahaifiyar ’yar jagorar Naira dubu 36 ke nan a shekara.
A haka Magajiya Dambatta ta rayu, har Allah Ya yi mata cikawa a ranar Juma’a 8 ga watan Oktoba, 2021.
An karrama Jafar Jafar bisa kokarinsa
Gidauniyar Grassroot Care and Aid Foundation (GCAF) ta karrama Jafar Jafar a matsayin Gwarzon Shekara shi da sauran wadanda suka taimaka wajen tabbatar da tallafin.
Shugaban Kungiyar, Ambasada Auwal Muhammad Danlarabawa ya ce, “Muna alfahari da ayyukan alheri na wadannan bayin Allah a wannan gagarumin aiki da suka yi wato Jaafar Jaafar da Musa Abdullahi Sufi da Ibrahim Sanyi-Sanyi da kuma Dokta namu.
“Wannan gangami da aka yi na taimaka wa Malama Magajiya Dambatta abin yabawa ne kwarai da gaske, mun yi farin ciki.
“Don haka ne wannan gidauniya ta yaba musu da shaidar karramawa ta Gwarazan Shekarar 2019 a wannan rana da addu’ar Allah Ya kara dafa musu a wannan kokari ya zama ya dore.”
Haka ma marubuci Tunde Asaju ya bayyana Jafar Jafar a matsayin Gwarzon Dan Jaridarsa na 2019, bisa kokarin da ya yi na ceto rayuwar Magajiya Dambatta.
Daga Lubabatu I. Garba, Kano, Isiyaku Muhammed da Sagir Kano Saleh