✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mafarauta sun yi wa ’yan bindiga kwanton bauna, sun ceto mutum 9 a Kaduna

Mafarautan sun cafke dan bindiga daya da ransa.

Mafarauta a kauyen Udawa na Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna sun samu nasarar cafke wani dan bindiga a wani daji da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Wani jagoran al’umma a yankin mai suna Muhammad Umaru ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da wakilinmu a ranar Lahadi.

Ya ce mafarautan sun kuma ceto wasu mutum 9 yayin kwanton bauna da suka yi wa ’yan bindigar da suka hana ruwa gudu a kauyen Udawa da kewayensa.

Bayanai sun tabbatar da cewa mafarautan sun yi wa ’yan bindigar kofar rago ce kwanaki kadan bayan harin da suka kai wa wasu matafiya a kan babbar hanyar ta Kaduna zuwa Birnin Gwari.

“An yi nasarar ceto wasu mutanenmu 9 daga hannun ’yan bindigar, inda kuma mafarautan suka samu nasarar cafke wani dan bindiga daya da ransa.

“A halin yanzu suna ci gaba da titsiye shi da tambayoyi gabanin su mika shi ga hukuma,” a cewar Umaru.

Aminiya ta ruwaito cewa, mafarautan sun fatattaki ’yan bindigar wanda a dalilin haka suka tsere suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su a maboyarsu.

Wannan lamari dai ya sanya farin ciki da annashuwa a fuskokin mazauna yankin la’akari da nasarar da aka samu.

Umaru ya ce mafarauntan za su rubanya kwazon da suke yi idan har aka yi musu tanadin motocin sintiri da za su rika kai-komo domin dakile ta’adar ’yan bindiga a yankin da kewayensa.

Kazalika, Umaru ya yaba wa jami’an tsaro da dangane da simamen da suka rika kai wa dajin bayan aukuwar wasu hare-hare biyu a jere a makon jiya.

ASP Jalige Mohammed, jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna da wakilinmu ya nemi jin ta bakinsa, ya ce har yanzu babu wani mutum da ake zargi da mafarautan suka gabatar, kuma ya ce ba a tuntubi rundunar game da lamarin ba.