Wasu mafarauta sun tsinci katinan zabe guda 320 a cikin wani kango a wani dajin da ke kan hanyar Elebele zuwa AIT a Karamar Hukumar Ogbia ta jihar Bayelsa.
Ana dai zargin wasu bata-gari da ake kyautata zaton ’yan dabar siyasa ne suka jibge katinan a kangon.
- Majalisa ta yi sammacin Emefiele bayan canjin Dala ya kai N700
- Dan Sanda ya yi wa ’yar dan uwansa fyade ta yi ciki
Kodayake ba a kai ga tantance makasudin yin hakan ba, amma wasu na zargin lamarin ba zai rasa nasaba da yunkurin wasu ’yan siyasar jihar na ganin sun lashe babban zaben 2023 mai zuwa ko ta wanne hali ba.
Da yake gabatar da katinan ga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a ofishinta da ke Yenagoa ranar Laraba, Kwamandan Kungiyar Mafarauta ta Jihar, Mosses Akanu, ya ce sun tsinci katinan ne a cikin wani kango.
Ya ce ’yan dabar sun gudu sun bar ladansu ne bayan sun hangi mafarautan da ke aikin sintiri a yankin.
Mosses ya kuma ce, “A yayin sintirin da na jagoranci gudanarwa a lungu da sakon dazukan a ranar Talata, mun sami nasarar ce sakamakon rahotannin da muka rika samu kan irin wainar da ake toyawa a ciki.
“Muna tsaka da sintirin ne sai muka ci karo da wancan kangon da wasu surutai na fitowa daga ciki, inda jami’anmu suka yi dirar mikiya a wajen don gano wadanda ke ciki.
“Shigarsu ke da wuya sai mutanen suka fara guduwa ta tagogi.
“Hakan ce ta sa muka shiga, inda muka tsinci wadannan katinan, shi ya sa muka ga ya kamata mu kawo wa INEC saboda ita ce ke da alhakin kula da su,” inji Kwamandan.
Da yake karbar katinan a madadin Kwamishinan INEC a jihar, Sakataren Mulki na hukumar zaben, Injiniya Okop Umobong, ya jinjina wa mafarautan kan kokarinsu na ganin an sami zaman lafiya a yankin da kuma kawo wa hukumar katinan.
Sakataren ya ce za su mika su ga Kwamishinan hukumar a jihar, Dokta Alex Harta, tare da ba da tabbacin za a gudanar da cikakken bincike don gano yadda aka yi katinan suka shiga daji.