✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mafarauta sun kashe Kwamandojin Boko Haram a Borno

An kashe kwamandan da mataimakinsa, yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga a jikinsu

’Yan banga sun kashe wani kwamandan kungiyar Boko Haram da mataimakinsa a wata arangama a kauyen Shaffa Taku da ke Karamar Hukumar Damboa a Jihar Borno.

Sun kuma kwato bindiga kirar AK-47 da babur da ’yan ta’addan suke amfani da su, yayin da wasu ’yan ta’addan da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.

mun yi artabu da su, inda muka yi nasarar kashe kwamandan da mataimakinsa, yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga a jikinsu,” inji wani shugaban ’yan bangar.

Shugaban kungiyar ’yan banga na Arewa maso Gabas (Sarkin Baka) da ke Karamar Hukumar Hawul ta jihar Borno, Alhaji Mohammed Shawulu Yohanna tare da tawagarsa suka ragargaji mayakan kungiyar a ranar Litinin din da ta gabata.

’Yan bangar sun kuma yi nasarar kashe ’yan ta’adda biyu, suka jikkata da dama tare da kama wasu mayakan kungiyar baiyar da ke kai abinci ga ’yan kungiyar.

Hakan na zuwa ne bayan kungiyar ta Boko Haram ta kashe manoma da dama a jihar ta Borno a kwanakin baya.

Wani yanki na Shaffa Taku dai yana tsakiyar Dajin Sambisa ne, maboyar ’yan kungiyar Boko Haram da suka addabi al’ummar Mandaragirau da ke Biu da kuma Sabon Gari a Damboa da sauran kauyukan Karamar Hukumar Askira-Uba cikin makonni biyu da suka wuce inda suke yin amfani da karfi kwatar haraji, da kuma wawure kayan abinci da dabbobi a yankunan.

A kwanakin baya ne dai shugaban mafarautan tare da tawagarsa suka cafke wasu ’yan Boko Haram da suke kai musu abinci tare da kwato miliyoyin Nairorin daga hannunsu a daya daga cikin kauyukan Karamar Hukumar Hawul, kafin ya mika su ga hukumomin bataliya ta 231 da ke Biu don tantance su.

Shugaban mafarauta na Arewa maso Gabas, Alhaji Yohanna a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai a Maiduguri ranar Talata ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Eh, mun yi aiki da bayanan sirri game da motsin ’yan ta’addan da suka addabi al’ummarsu cikin makonni biyu da suka gabata.

“Bayan samun labarin, sai na tattara tawagata na kai farmaki wurin da yamma a Shaffa Taku, wanda ba kowa a cikin garin Damboa.

“An yi sa’a mun ga ’yan ta’addan sun haura 20 a kan babura, mun yi artabu da su, inda muka yi nasarar kashe kwamandan da mataimakinsa, yayin da wasu da dama suka gudu da raunukan harbin bindiga a jikinsu.

“Mun kuma samu nasarar kwato babur daya da bindiga kirar AK47 daya daga hannun ’yan ta’addan; a halin yanzu na sanar da bataliyar soji ta 231 da ke Biu, kuma za mu hadu domin mika bindigar AK47 da aka gano da kuma babur din,” in ji Yohanna.