✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid za ta kara wa Ronaldo albashi daidai da Messi

Rahoton da kafar labarai ta ABC  a Sifen ta bayar a  ranar Litinin da ta gabata ya nuna kulob din Real Madrid na Sifen ya…

Rahoton da kafar labarai ta ABC  a Sifen ta bayar a  ranar Litinin da ta gabata ya nuna kulob din Real Madrid na Sifen ya fara yunkurin kara wa shahrarren dan kwallonsa Cristiano Ronaldo albashi. Idan karin ya tabbata, dan kwallon zai rika karbar albashin Yuro miliyan 9 kwatankwacin Naira biliyan 40 a shekara. Ke nan dan kwallon zai karbi adadin Yuro miliyan 30 kwatankwacin Naira biliyan 120 a tsawon kwantaraginsa da zai kare a shekarar 2021.

Sai dai kamar yadda rahoton ya nuna, Madrid ba yawan shekaru a kwantaragi za su kara wa Ronaldo wanda ya cika shekara 33 da haihuwa a ranar Litinin da ta gabata ba, a’a albashin ne za su kara masa da hakan zai sa ya yi kankankan da albashin Lionel Messi na FC Barcelona da kuma na Neymar da ke kulob din PSG na Faransa.

Sai dai masana harkar kwallo suna ganin hakan na da hadari ganin shekaru sun yi wa dan kwallon nisa, ba kamar Messi da Neymar da ba su kai shekara 30 ba, domin idan tauraruwarsa ta dushe a sauran shekarun kwantaraginsa to zai ci gaba da karbar  albashin ne ko bai yi kokari ba.

Ronaldo dai ya dade yana kokawa a kan a rika biyansa albashi daidai da Messi saboda irin namijin kokarin da yake yi wa kulob din Madrid.