✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid za ta bude sansanin horar da kwallo a Jihar Ribas

Kulob din Real Madrid da ke Sifen ya nuna sha’awar bude sansanin horar da matasa kwallo a Jihar Ribas.  Idan hakan ta yiwu cibiyar za…

Kulob din Real Madrid da ke Sifen ya nuna sha’awar bude sansanin horar da matasa kwallo a Jihar Ribas.  Idan hakan ta yiwu cibiyar za ta rika samar da matasan ’yan kwallo ne a ciki da kuma wajen Najeriya.

Bayanin haka na kunshe ne a lokacin da Gwamnan Ribas Nyesom Wike ya kai ziyara kulob din Madrid a karshen makon jiya inda ya gana da mahukunta kulob din da kuma wasu daga cikin ’yan kwallon kulob din.

A lokacin ziyarar, Gwamnan ya samu ganawa da shahararren dan kwallon kulob din Cristiano Ronaldo da kuma kyaftin Sergio Ramos.

A wata takarda da kulob din ya fitar a ranar Litinin da ta wuce, kulob din ya ce “Gwamna Wike ya kai ziyara ga kulob din Real Madrid inda ya tattauna da mahukunta kulob din da kuma wadansu daga cikin ’yan kwallon kulob din da suka hada da Cristiano Ronaldo da kuma Sergio Ramos.  Bayanin ya ce gwamnan ya kai ziyarar ce don a tattauna yiwuwar bude sansanin horar da matasa kwallo a Jihar Ribas ta Najeriya, kuma kulob din ya amince da tayin inda yanzu haka ya fara nazarin yadda hakan zai kasance”.

Gwamna Wike dai yana daga daga cikin masu goyon bayan kulob din Madrid da hakan ta sa yake sha’awar ganin ya janyo kulob din zuwa Jihar Ribas don ya bude sansanin horar da matasa kwallo.