✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid ta ware Naira Biliyan 42 don sayo Rashford da Eriksen

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Real Madrid na Sifen sun nuna mahukunta kulob din  sun ware zunzurutun Fam Miliyan 90 kwatankwacin Naira Biliyan…

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Real Madrid na Sifen sun nuna mahukunta kulob din  sun ware zunzurutun Fam Miliyan 90 kwatankwacin Naira Biliyan 42 don sayo ’yan kwallo biyu daga kulob din Manchester United da kuma na Tottenham a watan Janairu.

Kamar yadda rahoton da kafar watsa labaran wasanni ta  Sky Sport ta kalato a ranar Talatar da ta wuce, ta ce ’yan kwallon su ne Marcus Rashaford na Manchester United da aka kiyasta kudinsa a kan Fam Miliyan 50 da kuma Christian Eriksen dan kwallon kulob din Tottenham da aka kiyasta shi a kan Fam Miliyan 40.

Kulob din Madrid dai yana zawarcin Rashford ne ganin yadda ya yi kwazo a wasan da Ingila ta lallasa na Croatia a ranar Lahadin da ta gabata da ci 2-1 kuma idan ta same shi lallai zai karfafa ’yan kwallon gaba a kulob din yayin da  Eriksen kuma zai gaji Luka Modric ne da ake ganin nan ba da dadewa ba ne zai bar kulob din na Madrid.

Ana sa ran a watan Janairu mai zuwa (2019) ne kulob din zai sayo su idan aka bude kasuwar cinikin ’yan wasa.