Kocin kulob din Real Madrid na Sifen Zinedine Zidane ya ce kulob din ya shirya tsaf don karawa da na FC Barcelona a gasar rukuni-rukunin Sifen (La-Liga) a ranar Asabar 2 ga watan gobe idan Allah Ya kaimu. Wasan zai gudana ne da misalin karfe bakwai da rabi na dare agogon Najeriya kuma ana sa ran gidajen kallon kwallo a sassan duniya ciki har da Najeriya za su cika makil don kashe kwarkwatar idanu.
Zidane ya ce ganin yadda kulob din Madrid yake tashe a ’yan kwanakin nan ta sa ba ya shakkar haduwa da na Barca a wasa zagaye na biyu.
Kodayake FC Barcelona ta ba na Madrid tazarar maki 10 kawo yanzu a gasar, amma yana da muhimmanci Madrid ta samu nasara a wasan don farfado da martabar kulob din a idon duniya, inji Zidane.
An yi ittifaki wasa a tsakanin kulob din biyu da ake wa lakabi da El-Clasico shi ne mafi zafi a duniya. Hakan ta sa a duk lokacin da kulob din biyu suka hadu miliyoyin masoya kwallon kafa ne a sassan duniya ke rububin kallon yadda wasan zai kaya a akwatunan talbijin. Hasalima gidajen kallon kwallon kafa a Najeriya kan cika makil a duk lokacin da kulob din biyu ke gwabzawa. Masu gidan kallo sun nuna sun fi samun kudi ne a duk lokacin da ake wasa a tsakanin kungiyoyin biyu.
Sai dai a wannan karo da wuya wasan ya yi armashi kamar yadda ake zato ganin yadda Barcelona ta ba Madrid tazarar maki 10 a teburin gasar. Don haka ko Madrid ta samu nasara a wasan ba zai canja matsayin jagorantar gasar da FC Barcelona ke yi a halin yanzu ba.
Idan za a tuna, a watan Oktoban bara ne Barcelona ta bi Madrid har gida ta yi mata kaca-kaca da ci 4-0 a wasa zagayen farko, don haka a wannan karo Madrid za ta yi tattaki zuwa filin wasan FC Barcelona da aka fi sani da Nou Camp ne don yin wasa karo na biyu.
Barcelona ce ke rike da kofin La-Liga a halin yanzu kuma tana hankoron ganin ta yi sabi-zarce wajen sake lashe gasar a karo na biyu a jere.
’Yan kwallon gaba a kulob din Madrid irin su Cristiano Ronaldo da Gareth Bale da Karim Benzema ne ake sa ran za su gwabza da ’yan kwallon Barca irin su Lionel Messi da Neymar da Luis Suarez.
Madrid ta shirya wa wasan El-Clasico -Zidane
Kocin kulob din Real Madrid na Sifen Zinedine Zidane ya ce kulob din ya shirya tsaf don karawa da na FC Barcelona a gasar rukuni-rukunin…