✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madara ko omo?

Wani Bahadeje ne da ya je ci-rani birni, ya bukaci ya sha shayi sai ya je wajen wani mai tireda, ya nuna karamar jikkar omon…

Wani Bahadeje ne da ya je ci-rani birni, ya bukaci ya sha shayi sai ya je wajen wani mai tireda, ya nuna karamar jikkar omon ‘Good Mama’ ya ce a ba shi jikka daya. Shi ya zaci madarar gari ce ta leda. Ya amsa ya nufi teburin mai shayi, ya samu wuri ya zauna. Ya ce wa mai shayi a zuba masa amma kar a sa madara. Bayan an ba shi ruwan shayi, sai ya dauki kofi daya daban ya zazage farin omon nan, ya zuba ruwan shayi ciki ya fara shekawa. Kafin ka ce kwabo sai kumfa ta cika kofin har tana zuba. Shi kuwa sai ya ce: “Aradu wannan ai fitsarin jaki ne!”

Daga T. A. Buhari 08092055700