✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Macron ya ziyarci tsohuwar cibiyar IS a Iraki

Majalisar Dinkin Duniya za ta samar da tudun mun tsira a Kabul.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Mosul da ke zama tsowuhar cibiyar kungiyar da ke ikirarin jihadi ta IS a Iraki, kwana guda bayan da ya sha alwashin ci gaba da girke sojojin Faransa a kasar.

Ya kuma ziyarci wani coci da filin wani masallaci da kungiyar IS ta tarwatsa a shekarar 2017 domin nuna alhini ga dukkan al’ummomin da ke kasar Iraki.

A cikin wani jawabi da ya yi a cocin Our Lady of the Hour, wanda Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ke kokarin farfado da shi, Macron ya bukaci bangarorin addinai na Iraki da su hada kai don sake gina kasar.

“Za mu dawo da karamin Ofishin Jakadancin Faransa da kuma makarantu,” a cewarsa.

Macron ya kuma soki abin da ya kira a matsayin tafiyar hawainiya a ginin da ake yi na sake farfado da cibiyar ta Mosul, wurin da IS ta yi yakinta na karshe a cikin birni.

A shekarar 2017 ce aka sake kwato gari bayan ya shafe shekaru uku a hannun kungiyar IS, inda galibi Musulmai mabiya Sunna suka fi rinjaye.

Kawo yanzu kashi 30 zuwa 40 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiyar yankin an sake farfado da su a cewar wani jami’i a yankin.

Macron ya yi alkawarin Faransa za ta ci gaba da kasancewa a Iraki yayin wani taron yankin Gabas ta Tsakiya da aka karke a Bagadaza, wanda ya fi mayar da hankali kan yaki da ta’addanci da kuma tasirin mamayen da kungiyar Taliban ta yi a Afghanistan bayan janyewar Amurka.

“Duk wata shawara da Amurkawa suka yanke, za mu ci gaba da kasancewa a Iraki domin yakar ta’addanci,” a cewarsa yayin wani taron manema labarai na ranar Asabar.

A ranar Lahadi ce Macron ya ce Faransa da Burtaniya za su bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta samar da tudun mun tsira mai tsaro da aminci a Kabul domin kare ayyukan jin kai a Afghanistan.

Ya ce “tabbas wannan abu ne mai yiwuwa.”

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, ziyarar da Macron ya kai cibiyar ta kabilu da mabiya addinai mabanbanta a Iraki, ta nuna goyon bayansa ga Kiristoci a Gabas ta Tsakiya.

Kafin mamayar da Amurka ta jagoranta a shekarar 2003 wadda ta hambarar da mulkin abin da ta kira kama karya na Saddam Hussein, Iraki tana da tsirarun Kiristoci miliyan 1.5.

Sai dai a yanzu adadinsu ya ragu zuwa dubu dari hudu daga cikin akalla mutane miliyan 40 da ake da su bayan masu kaura daga kasar sakamakon rikice-rikice.

Faransa wacce ke daukar nauyin Makarantun Kiristoci masu amfani da harshen Faransanci a yanki, tana yunkurin fito da halin da Kiristoci ke ciki a Gabas ta Tsakiya da ma wasu tsiraru.

Macron ya kuma ziyarci Masallacin Mosul Al-Nuri, inda shugaban IS Abu Bakr al-Baghdadi ya ayyana kafa halifanci a shekarar 2014.

A watan Yunin 2017 ne IS ta tarwatsa sanannen ginin nan na karni na 12 yayin da Sojojin Iraki suka mamaye masu da’awa Jihadi a tsohon garin Mosul.

Macron ya tattauna da Barzani

A ranar Asabar ce Macron ya ziyarci Hubbaren Mabiya Shia na Imam Musa al-Khadm da ke gundumar Kadhimiya ta Arewacin Bagadaza tare da rakiyar Firaiministan Iraki, Mustafa al-Khademi.

Wannan ita ce ziyara ta farko a tarihi da wani Shugaban Faransa ya taba kai wa Hubbaren a cewarsa.

Haka kuma, a ranar Lahadi ce Macron ya gana da wasu matasan Iraki, da suka hada da ’yan kasuwa da dalibai a Jami’ar Mosul.

Daga bisani kuma Macron ya ziyarci Arbil, babban birnin yankin Kurdistan na Iraki mai cin gashin kansa, inda ya gana da Shugaban Kurdawa, Nechirvan Barzani.

Marcon ya shaida wa Barzani cewa Faransa za ta ci gaba da yaki da IS wanda alamu na damuwa ke bayyana suna sake yunkurowa a Syria da Iraki.

Kazalila, Shugaban na Faransa ya gana da iyalan mayakin Peshmerga da IS ta kashe, inda ya jinjina wa Kurdawa da ke bayar da gudunmuwar yaki da masu daawar Jihadi.

Gabanin rufe ziyarce-ziyarce a Iraki, Shugaba Macron ya kuma gana da sojojin Faransa na musamman a sansanin Grenier.