✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Macron ya lashe zaben Shugaban Faransa a wa’adi na biyu

Tuni dai abokiyar hamayyarsa, Marine Le Pen, ta amsa shan kaye a zaben

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya lashe zaben Shugaban Kasar a wa’adi na biyu, bayan ya doke babbar abokiyar hamayyarsa, Marine Le Pen a zagaye na biyu na zaben na ranar Lahadi.

Macron dai ya lashe zaben ne da gagarumin rinjayen kaso kusan 58 cikin 100, kamar yadda sakamakon farko-farko ya nuna.

A nata bangaren dai, ’yar takarar mai ra’arin rikau, Marine Le Pen, ta samu kaso 41.8 na kuri’un, kuma tuni ta amsa shan kaye a zaben.

Misis Le Pen ta sha alwashin ci gaba da gwagwarmayar siyasarta, inda ta ce ba za ta taba watsi da Faransa ba.

Har yanzu dai hukumar zaben kasar ba ta kai ga sanar da Macron a matsayin wanda ya lashe zaben a hukumance ba, sai zuwa nan gaba.

Emmanuel Macron dai zai kasance Shugaban Faransa na farko da ya lashe wa’adi na biyu tun zamanin Jacques Chirac a shekara ta 2002.

A zagaye na farko dai, Shugaba Macron ya samu kaso 28.1 cikin 100 na kuri’in, yayin da ita kuma Marine ta samu kaso 23.1, sai mai biye musu baya, Jean-Luc Mélenchon, wanda ya samu kaso 22.

Zaben dai ya maimaita kwatankwacin irin wanda aka fafata tsakanin ’yan takarar biyu a zaben 24 ga watan Afrilun 2017, wanda Macron ya lashe da gagarumin rinjaye.

Akalla masu zabe miliyan 48.7 ne suka yi rajistar zaben a fadin kasar.