Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi fatar kawo karshen tankiyar da ke tsakanin Rasha da Ukraine, bayan tattaunawa da Shugaba Vladimir Putin na Rasha a kokarin shawo kan rikicin bangarorin biyu ta hanyar diflomasiyya.
Macron wanda ya zauna nesa da Vladimir Putin a teburin tattaunawarsu cikin fadar Kremilin bayan isa Mosko ya sanar da manufarsa ta yayyafa wa rikicin kasar da takwarorinta na Turai ruwan sanyi, bayan tsanantar tankiyar bangarorin biyu da ya biyo bayan sake lalacewar alaka a tsakaninsu.
- Marigayi Sheikh Albani: Ayyukan alherinsa ne abin koyi da yabawa
- Dalilan da rikice-rikicen Kudancin Kaduna suka ki ci suka ki cinyewa
A cewar Macron ziyarar tasa za ta zamo mafarin sassautowar bangarorin biyu, wato Rasha da abokanta kasashen Yammacin Turai.
Ya ce gamsasshiyar amsa daga Mosko za ta zamo mai amfani ga dukkan bangarorin biyu da Turai baki daya.
Shugaba Putin wanda ya kira Macron da ‘‘Emmanuel dinsu,’’ ya ce Rasha da Faransa suna aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiyar Turai, kuma abin yabawa ne irin kokarin da Shugaban Faransar ke yi a yanzu don warware wannan matsala.
Gwamanatin Ukraine ta ce, damar sasanta rikicinta da Rasha ita ce ta hanyar diflomasiyya maimakon shirin kai hari Amurka ta ce sakamakon nazarin da ta yi a kan bayanan sirrin da ta tattara na nuni da cewa Rasha na kara azama don mamaye Ukraine, kuma yanzu haka ta girke kashi 70 na sojin da take bukata don kaddamar da hari.
Jami’an Amurka sun ce Putin yana bukatar sojoji dubu 150 don aiwatar da mamayar, kuma sun ce hakan na iya kaiwa ga karbe babban birnin kasar, Kyiv tare da hambarar da Shugaba Bolodymyr Zelensky a cikin sa’o’i 48.
Za mu sa kafar wando daya da Rasha —Amurka
Amurka ta sake yin kashedin cewa Rasha za ta kai samame ta sama a kan Ukraine a cikin ’yan kwanaki masu zuwa, kamar yadda mai bada shawara a fannin tsaro na kasar Jake Sullivan ya bayyana, yana mai kira ga Amurkawa da ke Ukraine da su fice a cikin sa’o’i 48.
A yayin da yake watsi da ikirarin cewa babu yadda Rasha za ta kadamar da wani hari alhalin aminiyarta China na karbar bakuncin gasar wasanni na Olympics, Sullivan ya ce wannan harin ma na iya faruwa ne kafin a Karkare gasar a ranar 20 ga watan Fabrairu.
A yayin da yake jaddada cewa babu masaniya ko shugaba Vladimir Putin ya yanke shawara a game da hakan, Sullivan ya ce Amurka ta shirya mayar da martini ga kowane irin abin da Rasha ta taho da shi.
Wannan bayanin na Sullivan na zuwa ne jim kadan bayan da shugaba Joe biden na Amurka da wasu shugabannin kasashen Turai 6, da jagororin kungiyar tsaro ta NATO suka gudanar da wata tattaunawa a kan rikici mafi muni tsakanin Rasha da kasashen yamma tun bayan yakin cacar baki.
Amurka ta bukaci ’yan kasarta su fice daga Ukraine
Shugaba Biden ya yi kira ga ‘yan kasar Amurka mazauna Ukraine da su gaggauta ficewa daga kasar ba tare da bata lokaci ba.
To sai dai kuma, shugaba Biden dake zantawa da gidan talbijin na NBC, ya ce: “Amurkawa su fice daga Ukraine nan take, lamurra za su iya dagulewa cikin sauri, domin sojojin Amurkar ba za su samu damar zuwa kwashe su ba, idan lamari ya rincabe.”
Shugaban Biden ya ce, ba zai aike sojoji kwashe Amurkawan ba ne saboda gudan haifar da “Yakin Duniya”
Hakan na zuwa ne bayan da Rasha ta fara wani atisayen soja tare da makociyarta Belarus, matakin da shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya bayyana, a matsayin yanayi mai cike da hatsarin gaske ga tsaron nahiyar Turai, mataki mafi girma da aka gani, tun bayan kawo karshen yakin cacar baka.
Rasha dai ta sha musanta cewa tana shirin afka wa Ukraine duk da cewa ta jibge dakaru dubu 100 a kusa da iyakarta.