✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maciji ya sare shi a hanya bayan ya gudo daga hannun masu garkuwa da shi

matashin dai da ne ga babban limamin ’Yangoji, Abdullahi Abubakar Gbedako.

Daya daga cikin mutanen da ’yan bindiga suka sace a garin ’Yangoji da ke yankin Kwali a Babban Birnin Tarayya Abuja, Usman Abubakar, ya gamu da iftila’in saran maciji bayan ya gudo daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

Aminiya ta rawaito cewa matashin, mai kimanin shekara 22, wanda da ne ga babban limamin na ’Yangoji, Abdullahi Abubakar Gbedako, an sace shi ne tare da mahaifin nasa da kaninsa a gidansu da ke yankin makonni biyu da suka gabata.

Daya daga cikin iyalan matashin wanda bai amince a bayyana sunansa ba ya ce Usman ya sami damar gudowa daga hannun masu garkuwar ranar Alhamis, amma maciji ya sare shi a hanya.

Ya ce, “Yanzu haka yana nan ana yi masa maganin gargajiya a wani wajen da ba zan iya bayyanawa ba saboda dalilai na tsaro.

“Ka san har yanzu akwai mahaifinsa da kaninsa a hannunsu,” inji majiyar

A cewar majiyar, yanzu haka iyalan mutumin na can suna ta fadi tashin neman yadda za su hada kudaden fansar babban limamin da dansa.

Masu garkuwar dai na neman a biya su Naira miliyan 10 kafin su sake su.