Daya daga cikin kwamandojin kungiyar ISWAP ya mutu a Jihar Borno, sanadiyar sarar da maciji ya yi masa.
Kwararren mai masani kan yaki da tayar da kayar baya a gabar Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan.
- JAMB ta kayyade mafi karancin makin samun gurbin karatu a bana
- Dalilin da na dakatar da Gwamnan CBN —Tinubu
Makama ya ce kwamandan na ISWAP da ake kira da Kiriku, ya mutu ne a ranar Juma’a kwanaki uku bayan sarar macijin a maboyarsu da ke yankin Karamar Hukumar Damboa.
Ya ce mutuwar ta Kiriku na da nasaba da rashin kulawa tun bayan sarar da maciji ya yi masa.
Kafin mutuwarsa, Kiriku ya jagoranci kai hare-hare a yankin Jiddari da ke Chiralia, yankin da ke zaman matattarar Boko Haram da kuma ISWAP.
Haka nan ya jagoranci kai harin kwanton bauna kan jami’an sojojin da ke aiki a karkashin rundunar Operation Hadin Kai a jahar Borno.