✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na dakatar da Gwamnan CBN —Tinubu

Ai yanzu Emefiele yana hannun hukuma kuma za a dauki mataki a kansa.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya magantu kan dalilinsa na dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele daga mukaminsa.

Ana iya tuna cewa, a ranar 9 ga wannan wata na Yuni ne wata sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar ta ce an dakatar da Emefiele ne domin a gudanar da bincike sannan kuma ya sauya fasalin harkokin kudi a kasar.

Daga bisani kuma Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta cafke Emefiele a Legas ta kuma dawo da shi Abuja inda har kawo yanzu yake ci gaba da shan titsiye.

Da yake jawabi a wani taron zauren musayar ra’ayi da ’yan Najeriya mazauna Faransa, Shugaba Tinubu ya ce bangaren harkokin kudi na Najeriya ya durkushe a karkashin jagorancin Emefiele.

A cewar Tinubu, da yawa daga cikin wadanda ke zaune a wajen Najeriya ba sa iya aika wa iyayensu ko ’yan uwansu kudi saboda yadda aka dagula lamura kasauwar canjin kudi.

Sai dai Tinubu ya ce “a yanzu duk wannan ya kau ya zama tarihi.

“A nan baya kadan tsarin harkokin kudi ya lalace. Mutane kadan ne suka tara buhunan kudi sannan ku kanku kun daina aika kudi gida ga iyayenmu talakawa. Amma yanzu duk wannan ya zama tarihi.

“A yanzu mutumin yana hannun hukuma. Akwai matakai da ake dauka game da hakan. Za su warware komai.

“Muna da kalubalen tsaro a kasar nan. Watakila ta haka ne suke haifar da matsalar tsaron tun fil azal; dole ne mu yi nazari sosai a kan komai. Za mu canza tsarin kudi dai zai yi muku aiki,” in ji Tinubu.