✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harsuna 20 da a za a fassara hudubar Arafa ta bana

Hausa ne kadai harshen da ya samu damar shiga jerin harsuna a duk fadin Najeriya.

Mahukunta Masallatan Alfarma na kasar Saudiyya, sun sanya Hausa a cikin jerin harsuna 20 da za a yi amfani da su wajen fassara hudubar ranar Arafa ta bana.

Shafin Haramain Sharifain ne ya tabbatar da hakan cikin wani sako da ya wallafa ranar Asabar a shafinsa na Facebook.

Hakan dai na nufin Hausa ne kadai harshen da ya samu damar shiga jerin harsunan a duk fadin Najeriya.

A shekarun bayan nan dai an rika fassara hudubar ranar Arafa cikin harsuna daban-daban, inda kusan shekaru uku da suka gabata harshen hausa ya samu shiga.

Ga jerin harsunan da za a yi amfani da su wajen fassarar hudubar ta bana:

1. Turanci
2. Faransanci
3. Malay
4. Urdu
5. Persian/ Farsi
6. Chinese
7. Turkish
8. Russian
9. Hausa
10. Bengali
11. Swedish
12. Spanish
13. Swahili
14. Amharic
15. Italian
16. Portuguese
17. Bosnian
18. Malayalam
19. Filipino
20. German