Tsawon shekara biyar ke nan ana gudanar da bikin Ranar Hausa ta Duniya a tsakanin kasashen Afirka da suke da Hausawa da kuma wasu sassan duniya da ake amfani da harshen Hausa.
Bikin da ake yi a duk ranar 26 ga Agusta, duk shekara akwai taken da ake ba wannan rana a mabambantan kasashen da suke biki.
- Hausa ne harshen da aka fi amfani da shi a Afirka ta Yamma —Bincike
- NAJERIYA A YAU: Ranar Hausa Ta Duniya: Yadda Harshen Uwa Zai Taimaka Wurin Inganta Ilimi
- Abubuwan da ya kamata ku sani a kan ranar Hausa ta Duniya
Sai dai a bana taken bikin ya zo iri daya a tsakanin kasashen, wato, ‘Zaman Lafiya da Kaunar Juna’ inda dukkan kasashen suka mayar da hankali a kan yin addu’o’in samun zaman lafiya a kasashen da suke fama da matsalolin tsaro da sauransu.
Wakilin Aminiya wanda ya je kasar Burkina Faso don halartar taron na bana, da za a gudanar yau ya tuntubi wasu masu shirya taron a kasashen Afirka ta Yamma don jin tsare–tsaren da suka yi a bikin na yau.
Babban abin da ya fi jan hankali a taron na bana shi ne, mahalarta taron za su fi mayar da hankali ne a kan yi wa Najeriya musamman jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalolin tsaro da zubar da jini da sauran kasashen da suke fama da matsalar irin su Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar addu’o’in zaman lafiya.
Gamayyar kungiyoyin bunkasa al’adu da yada harsuna Afirka a duniya mai suna ‘Gidauniyar Zumunci ta Duniya (GIZU), wadda ta hado kasashen Najeriya da Nijar da Burkina Faso da Togo da Kamaru da Chadi da Senegal da Gini Bissau da Benin ne ke jagorantar taron.
Kungiyar wadda ta samo asali daga taron baje kolin al’adun Hausa na ranar 14 ga Afrilun 2017 a garin Wagadugu a karkashin Kungiyar “Makaranta,” da ta sake zama a garin Yamai a ranar 16 ga Mayun 2017 don samar da kungiyar ta duniya.
Kuma a taron ne aka yanke hukuncin cewa duk da dimbin harsunan da ke akwai a kasashen kungiyar, harshen Hausa ne harshen da za a rika amfani da shi a duk lokacin wani taron kungiyar wadda babbar hedkwatarta ke birnin Yamai.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi jagoran kungiyar Alhaji Garba Sani, kan yadda kasashen da za su gudanar da taron suka dauki take daya, ya ce, “Wannan mataki na yin addu’o’in samun zaman lafiya da kaunar juna da muka dauka ya biyo bayan shawarar da uban kungiyar Mai martaba Sultan na Damagaram Alhaji Umar Sanda ya ba mu na yin hakan lura da halin da kasashenmu ke ciki na rashin tsaro da rabuwar kawuna.
Hakan ne ya ba mu kwarin gwiwar yin nazari a kungiyance muka aminta da hakan maimakon yin wasu shagulgula.
Duk wani dan Afirka yana cikin damuwa kan yadda harkar tsaro ta tabarbare musamman a Arewacin Najeriya wadda dole abin ya shafe mu.
Sannan ga Burkina Faso da sauransu. Dubi abin da ya faru a Sudan, abin babu dadin ji.”
Can a kasar Senegal an karbi bakuncin Kungiyar Nigeria Arewa Community da ke kasar Guinea-Bissau bisa jagorancin Alhaji Sule Adah a Dakar.
Shugaban Kulob Zumunci na Senegal, Alhaji Aliyu Waisu ya ce, kungiyar ta Guinea-Bissau ta nemi zuwa Senegal taron ne don kara dankon zumunci da gudanar da addu’o’i tare da gabatar da kasidu da jawaban da za su kara hada kan al’ummar Afirka, musamman Hausawan da wasu ke ganin an mayar da su baya a fannoni da dama.
Jama’a da dama da Aminiya ta tuntuba sun ce, da za a ci gaba da koyar da dalibai a makarantu sauran darussa da harshen Hausa lallai da al’ummar kasashen Afirka sun ci gaba.
Dokta Aliyu Idris Funtuwa (Maikaji), Shugaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Jihar Katsina a Najeriya ya yi tsokaci a kan wannan batu duba da yadda aka yi wa taron Ranar Hausa ta Duniya shiri mai kyau.
Ya waiwayi baya kan yadda aka fara yin gwaji a wannan tsari na koyar da dalibai daga firamare harshen gida, fa’ida da abubuwan da suka biyo baya kafin a raba makarantun sakandare gida biyu, wato shekara 3 karama da 3 a babba.
A tattaunarwa da shi ta waya, Dokta Aliyu ya ce, “An taba yin gwaji a lokacin Minista Farfesa Fafunwa inda aka fara da yankin Yarbawa aka fara koyar da darussa a harshen uwa daga ajin firamare na 1 zuwa 3 kafin a kawo tsarin karama da babbar sakandare, amma abin ya ci tura domin daga cikin yankunan da ba su yi hakan har da Arewa.
Kusan ma abin sai ya nemi ya zama kabilanci wanda hakan ya sa aka kawo batun amfani da manyan harsuna uku da muke da su, wato Hausa da Yarbanci da Ibo.
Amma in za a daure a aiwatar da tsarin zai yi ma’ana, sai dai zai kawo rabuwar kawuna a tsakanin ’yan kasa, saboda in aka duba a nan Arewa muna da kabilu ko harsuna sama da 100 duk da cewa suna jin Hausa.”
Dokta Aliyu ya yi bayani kan yadda amfani da harshen uwa ya yi tasiri a kasashe irin su Indiya da Japan da China da sauransu ta yadda suka zamo abin misali a fagen ilimi.
“Ka san mu Hausawa babbar matsalarmu dogaron da muka yi tare da daukar harsunanan Ingilishi da Larabci da muhimmanci fiye da namu.
“Har gobe dan Najeriya ba ya kallon wadannan harsuna a matsayin baki. Misali, idan kana Ingilishi ba za a ce kana wani yare ba kamar yadda za ka yi Yarbanci.
“Kawai ana kallon ka wani gogagge ko wayayye mai ci gaba ta fuskar ilimi. Haka abin yake in kana Larabci ka gama da Bahaushe saboda yana kallon ka ta fuskar addini.
“Baya ga wadannan harsuna biyu duk wani harshe da ka yi amfani da shi ci baya ne. Wannan ita babbar matsalarmu.
“Ka dubi iyaye masu kai ’ya’yansu makarantun kudi, babbar bukatarsu yaro ya iya Ingilishi, ko da bai san komai a sauran darussa ba. Alhali Ingilishi yaren wasu ne,” inji shi.
Malamin ya ce, harshen uwa shi ne mafi dacewa wajen bunkasa ilimi ba na aro ba, wanda in ana maganar neman ilimi da na aro aiki biyu ake yi, koyon bakon harshe da abin da ake son a koya.
Ya ce, hakan ke sa a bar kasashenmu na Afirka a baya a fannin ci gaban zamani da kimiyya da sauransu, saboda wadancan ‘yan mulkin mulkin mallaka sun gane cewa mun fi daukar harshensu da muhimmanci fiye da namu wanda kuma Bahaushe shi ne kan gaba ta wannan fuska.