Lami Sadiq ta zama mutum ta farko da za ta shugabanci Sashen Binciken Kwakwaf na Rukunin Kamfanonin Media Trust, masu jaridun Daily Trust da Aminiya da Trust TV da kuma Trust Radio.
Matashiyar ’yar jarida Lami Sadiq, ta samu matsayin Editan Binciken Kwakwaf Rukunin Kamfanin ne bayan ta yi wa sauran wadanda suka nemi mukamin fintinkau, da kwarewarta, musamman a fannin.
- 2023: Al-Mustapha: Na hannun daman Abacha da ke son haye kujerar Buhari
- Obasanjo ya tafka babban kuskure kan goyon bayan Peter Obi – Sule Lamido
“Za ta jagoranci ’yan jaridar zamani da sauran ma’aikata wajen tsarawa da kuma aiwatar da zurfafan binciken da suka dace da bukatun masu bibiyar mu.”
“Rahotannin da za ta jagoranci samarwa za su kasance masu tasiri ga masu bin mu ta jarida, intanet, talabijin da kuma rediyo,” in ji sanarwar Babban Edita kuma Babban Daraktan Gudanarwar Aikin Jarida da Fasahar Zamani na kamfanin, Naziru Mika’ilu Abubakar.
Ya bayyana cewa sabuwar Editar Binciken Kwakwaf din za ta fara aiki a sabon ofishinta ne ba tare da bata lokaci ba.
Lami Sadiq zakakurar ’yar jarida ce da ta yi rahotannin binciken kwakwaf da suka lashe kambuna, sannan ta sha samun tallafi domin gudanar da binciken kwakwaf a tsawon shekaru.
Mamba ce a Cibiyar Aikin Jaridar Binciken Kwakwaf ta Wole Soyinka da kuma Cibiyar Dubawa da ke yaki da Labaran Karya.
A shekarar 2019, Lami Sadiq ce ta lashe kambun Zakaran ’Yan Jarida na Jihar Filato.
Sannan ta lashe kyautar wanda ya fi kowa bajinta a kamfanin Media Trust da take aiki.
Kafin sabon mukamin nata, ta kasance Mai Kula da Ofisoshin Daily Trust da ke Jos da kuma Kaduna.
Da yake jinjina mata, Malam Naziru ya ce, “Gogaggiyar ’yar jarida Lami Sadiq za ta kawo kwarewarta da kuma bajintar shugabanci a sabon matsayin da ta samu.”
Lami Sadiq ta yi karatun digirinta na farko da na biyu ne a fannin aikin jarida a Jami’ar Jos.