✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

MacArthur ta tallafa wa CITAD don wayar da kai game da rigakafin COVID-19

MacArthur ta ba da tallafin don yaki da COVID-19 a Arewacin Najeriya.

Gidauniyar MacArthur da ke kasar Amurka ta bai wa Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma (CITAD), tallafin kudi don wayar da kan al’umma game da alfanun rigakafin cutar COVID-19 a Arewacin Najeriya.

Gidauniyar ta MacArthur ta sanar da bayar da tallafin Dalar Amurka miliyan 80, a matsayin taimokonta a kan yaki da cutar da ta addabi duniya.

  1. An cafke uba ya yi wa ’ya’yansa uku fyade
  2. Zulum ya yi wa matasa masu neman aikin soja alawus a duk wata

Shugaban gidauniyar, John Palfrey, ya bayyana cewa la’akari da halin da aka ciki da kuma yadda annobar ta yi tasiri ga abubuwan da suka shafi rayuwar al’umma kuma suna bukatar farfadowa ya sanya ta bayar da tallafin.

Palfrey ya ce gidauniyar ta himmatu wajen ganin bayan annobar ta hanyar bayar da tallafi domin farfado da wuraren da cutar ta yi wa illa, da kuma ci gaba da wayar da kan al’umma domin ganin sun karbi rigakafin cutar.

CITAD na daya daga cikin kungiyoyin da suka samu tallafin na yaki da COVID-19, tare da wayar da kan al’umma a kan alfanun da ke tattare da rigakafin cutar.

Tuni Kwamitin Fadar Shugaban Kasa kan yaki da COVID-19 ya ware jihohi shida da Birnin Tarayya, a matsayin yankuna mafiya hadari da ake fargabar sake barkewar cutar a karo na uku.

Jihohin sun hada da Legas, Oyo, Ribas, Kaduna, Kano, Filato da kuma Birnin Tarayya, Abu.

COVID-19 dai ta jefa tattalin arzikin kasashen duniya cikin mawuyacin hali ciki har da Najeriya, inda abubuwa da dama suka samu koma-baya.