Assalamu Alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, za mu ci gaba da bayani kan mataki na biyu da maigida zai hau don bude sha’awar uwargidansa, watau koyi Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarshi kuma ya amfanar da su, amin.
Babban kuskure!:
Da yawan Magidanta Musulmi, su na tsananin son Manzon Allah SAW, Suna kishinsa, suna alfahari da shi, suna begen shi, amma sai dai kash! Da yawansu kuma ba su yin kokari wajen cikawa da raya Sunnar shi a cikin rayuwarsu ta yau da kullum, musamman kuma a cikin rayuwar aure. Annabinmu SAW, ba masoyin maigida irinsa, ba wanda ya kai shi iya nuna kula ga iyalinsa, ba kamarsa wajen iya nuna kauna da soyayya; ba kamarsa wajen iya fadar kalmomi masu kyau, masu dadi; masu sa nishadi cikin zuciya, amma sai dai, kaiconmu, da ba mu yin koyi da wadannan kyawawan dabi’u na manzonmu SAW, ba mu bin umarnin kyawawan abubuwan da ya yi umarni da aikata su, illa dai muna yin abin da ya yi mana dadi kadai daga ciki, muna yin abin da mu ka ji za mu iya yi cikin sauki; ba mu dagewa mu yi masu wuyar yin; koda yaushe sai mu sai mu fake da: “Iyakar iyawata ke nan; Ai Allah ba Ya dora ma rai wani abu sai wanda za ta iya!”
Misali, a harka ta auratayya, kowa zai yi ta kwadayin ya yi aure, ai raya sunnar Annabi SAW ne; ai cikamakon addini ne; amma in an yi auren, sunnar ibadar auren kadai ake kokarin rayawa, amma ba a dubi ga aiwatar da irin abubuwan da Annabi SAW ya yi cikin rayuwar auratayyarsa, irinsu tsananin kyautatawarsa ga iyalinsa; tsananin hakurinsa da su; nuna soyayyarsa SAW ga iyalansa cikin hikimomi da hanyoyi masu kayatarwa; irin yadda ya yi tsananin adalci tsakaninsu, da sauransu, wadanda su ne ke zakaka sunnar ibadar aure da kuma rayuwar auren gaba dayanta. Da fatan Allah Ya bamu ikon rayar da dukan sunnonin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a cikin rayuwarmu ta yau da kullum musamman a cikin rayuwar aure, don kyautata rayuwar iyalanmu, wanda shi ne tushe na gina al’umma mai kyau.
Tambaya daya da ba mu cika yi ba!:
‘Shin Ya Annabi SAW Ya Ke hulda da matarsa RA?’ Ita ce tambaya da ba mu damu da ba mahimmaci ba balle har mu dage mu aiwatar da amsarta. Yawancin musulmi na wannan zamani, akwai mu da kokarin yin ibadodinmu kamar yadda muka ji an ruwaito cewa ga yadda Annabinmu Sallallahu Alaihi Wasallam yake yi; musamman manyan ibadoji irinsu sallah, azumi, hajji, da sauransu. Amma abin mamakin, wajen zamantakewa irin ta aure, ba mu cika bayar da muhimmanci kan sanin ‘shin ya Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yake hulda da iyalansa RA ba?’ domin mu yi irin yadda ya yi, sai dai mu yi ta yin yadda muka ga ana yi a al’adance, alhali, shi ma aure ibada ce babba, har ma a wani kaulin an kira shi da rabin addinin ma gaba daya, to shin ya kamata mu rika sakaci wajen raya sunnonin auratayya kuwa?
Ina mana tuni da babbar murya da mu sani, su ma wadannan abubuwa na cikin rayuwar aure sunnoni ne masu kyau kuma masu karfi, don haka ya zama wajibi ga duk musulmin ya yi kokarin rayar da su, musamman in aka yi la’akari da dimbin lada da ribar da ke cikin yin haka din a duniya da ranar gobe kiyama, da fatan Allah Ya ba mu ikon dagewa, amin.
Magidancin da babu kamarsa!
Kamar yadda ya kasance mafi daukaka cikin bayin Allah, kuma fiyayye cikin dukan halittun Allah, to haka kuma a wajen zamantakewar aure, babu wanda ya kai sa gwanancewa wajen zamantakewar aure Sallallahu alaihi wa Sallam. Shi don kansa ya sanar da Aishah Allah Ya kara mata yarda cewa shi ne mafificin maigida. Don samun kari da gwanancewa wajen iya hulda da uwargida, da fahimtarta da kyautata mata, sai a biyo bayani na gaba in sha Allah.
Mako mai zuwa In sha Allah da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.