✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mabarnata ne ke rura wutar fitina – Ibrahim Magu

Yaya rashin tabbatar maka da shugabancin Hukumar EFCC ke shafar aikinka, shin yana kashe maka gwiwa ko yaya kake ji? Na fada a baya cewa…

Yaya rashin tabbatar maka da shugabancin Hukumar EFCC ke shafar aikinka, shin yana kashe maka gwiwa ko yaya kake ji?

Na fada a baya cewa daga lokacin da aka ba ka aiki, ka mayar da hankali a kai, ba tare da lura da cewa wani yana gode maka ba ko a’a. Don haka babu abin da yake kashe min gwiwa, ko ka ga alamar rashin karsashi daga gare ni? Babu abin da yake hana ni barci.

Ba ka jin akwai wani abu da ya kamata ka yi wanda rashin tabbatar da kai ya hana ka yi?

Babu, domin ina da ikon zartarwa wanda rashin tabbatarwar ba ta dauke min wannan ikon zartarwa ba.

 

Me kake ji ya hana a tabbatar maka da shugabancin?

Ina jin aikinku ne ku gano haka. Ni ba sanata ba ne, ku ya kamata ku fi ni sani.

 

Shin kana jin kana samu goyon baya daga sauran hukumomin tsaro?

Batun shi ne muna yin wannan aiki ne saboda jama’a, don haka ya kamata a fadakar da jama’a su fahimci cewa cin hanci da rashawa da almundaha laifi ne, domin jama’a ne kawai za su yaki almundahana.  A yau na ziyarci Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), na roki shugaban hukumar ya tattaro mana dukan shugabannin jami’o’in kasar nan wuri guda domin fadakar da su kan almundahana. Domin akwai almundahana a sosai a jami’o’in kasar nan a abin da ya shafi harkokin karatu da ba dalibai gurbin karatun da sauransu. Muna son mu roke su su kirkiro wasu sassa da za su yaki cin hanci da rashawa da almundahana. Sannan ko me dalibi yake karantawa za a samu bangare na kwas da za a nuna muhimmancin yaki da almundahana, ya alla yana karanta kimiyyar siyasa ce ko ko wane darasi. Hakan zai taimaka wajen kawar da almundahana.

 

Akwai masu ganin cewa matsalar ita ce, babbar matsalar Najeriya ita ce mutanen da ake tuhuma da almundahana a karshe suna komawa su rika yawonsu kamar ba komai. Ga shi yanzu kana maganar fadakarwa, ba ka ganin kana kawar da hankalinka ne saboda ’yan Najeriya sun fi son su gana ana hukunta wadanda aka kama?

Wato muna hukuntawar. Amma mun dauki batun fadakar da jama’a ne, domin rigakafi ya fi magani. Zuwana nan wani bangare ne na yin rigakafi a fahimtar da jama’a su yaki almundahana.  Wannan ne zuwana na biyu a nan, kuma burinmu a fadakar da jama’a. Domin ba kullum ne za a kama mutane a hukunta sub a, ko a yanzu da muke magana akwai wadanda aka hukunta da wadanda suke fuskantar hukunci. Akwai bukatar a rika fadakar da jama’a, sau nawa ina zuwa nan, duk bangare ne na fadakarwar.

 

Me kake ji za ku yi ku hukunta yaki almundahana ta wajen hukunta wadanda suka aikata almundahanar musamman ’yan siyasa don ya zame darasi ga saura?

Aikina ya tsaya ne a kan bincike da kai batun gaban kotu tare da gabatar da shaidu da hujjoji a lokacin shari’ar. Kuma muna da matasan jami’ai wadanda suke gabatar da kara a gaban kotuna. To amma matsalar da muke fuskanta ita ce, sai ka ga a shari’a daya mun fuskanci manyan lauyoyi 30. Misali ina da wata shari’a da manyan lauyoyi (SAN) wajen 30 suka tsaya masa. Yaya wani zai dauki manyan lauyoyi 10 zuwa 30 su tsaya masa, kuma irin wadannan lauyoyin sukan yi ta zare wa alkalai ido suna takura musu.

 

Me za ka ce shi ne babban abin da ke kawo maka matsala?

Shi ne almundahana yana yakarmu. Masu almundahana da maciya hanci da rashawa, suna juyowa suna yakarmu. Masu almundahana sun ma mallake wasu kafofin watsa labarai.

 

Mene ne babban kalubalen da kake fuskanta?

Babban kalubalen shi ne cin hanci da rashawa na yakarmu. Kuma babbar matsalar mutane suna girmama maciya hanci da rashawa da masu almundahana. A kasar nan kawai za ka ji wani ya ce maka almundahana ba laifi ba ne ba barna ba ce, wannan kuskure ne! A kasar nan ne kawai a duk duniya ake fadin haka.

 

Me ya sa yake da muhimmanci hukumar sanya ido kan harkokin kudade ta kasance a karkashin Hukumar EFCC?

Saboda Hukumar EFCC ita ce hukumar tabbatar da doka da ta fi cancanta, tana daya daga cikin hukumomin tabbatar da bin doka. Idan ka dubi shawarar da kwamitin musamman kan harkokin kudi ya bayar, ya ce, mafiya ingancin hukumomin sanya ido kan harkokin kudi a duniya su ne wadanda suke karkashin irin wannan hukuma. Misali kasar Jamus, an kori Jamus daga rukunin Egmont Group (wani rukunin cibiyoyin sanya ido kan harkokin kudade don yaki da safarar kudade ko karkatar da su zuwa ga kungiyoyin ta’adda).  To muna aiki ne don yadda za mu tabbatar da wannan ka’ida kuma na san wadannan ka’idoji, saboda na yi aiki da Egmont Group kuma na sha halartar tarurrukansu. Abin da kawai ake nema daga gare mu shi ne a gyara dokar ta shafi wannan bangare don ya dace a kirkiro sashin sanya ido kan harkokin a matsayin wani bangare a karkashin Hukumar EFCC kuma a ba shi cikakken ikon gudanar da ayyukansa ta fuskar kudaden gudanar da aiki da na harkokin ma’aikatansa. A baya-bayan nan lokacin da Jamus ta karya wannan ka’ida ta cire bangaren sanya ido kan harkokin kudi daga Hukumar ’Yan sanda ta mayar karkashin Hukumar Kwastam, sai aka kori Jamus daga Egmont Group, tilas Jamus ta mayar da wannan hukuma karkashin hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ke karkashin ’yan sanda. To in ba mu gyara dokar ba, zai zamo sai mun koma mun sake gini tun daga tushe ken an, mu koma mu auna mu daddale kafin a kira mu a rukunin Egmont Group.

 

Hukumar EFCC ta kai Madam Patience Jonathan kan Dala miliyan biyar da doriya tana neman a mika wa gwamnati mallakin wannan kudi da take ganin an same su ne ta haramtacciyar hanya. Me ya sa ba za ta kama wadda ake zargi da mallakar kudin ba?

Ka je ka dubi bayanan abubuwan da muke nema a takardun da muka gabatar a gaban kotu. Mun yi bayani dalla-dalla kan takardar rantsuwar da muka gabatar a gaban kotun.

Muna bin abubuwan ne mataki-mataki.

 

Yaushe ke nan za ku gayyaci Patience Jonathan zuwa Hukumar EFCC?

Wasu abubuwa ne suke jawo wasu, muna bin abin ne mataki-mataki.

 

Wadanne ne matakan?

Suna nan a cikin takardun da muka gabatar a gaban kotu.

 

Ko hukumar tana da hadin gwiwa a tsakaninta da takwarorinta na wasu kasashen duniya?

Sosai ma, ko a yanzu haka mutane daga Kamaru daga hukumarsu ta yaki da cin hanci da rashawa za su kawo mana ziyara gobe (shekaranjiya Laraba). Kuma mutanen Nijar ma za su zo. Sashin sanya ido kan harkokin kudi na Najeriya ya fi kowanne bin ka’ida a Afirka. Babu wata kasa da ta kai ta Najeriya inganci.  Don haka Kamaru za su ziyarce mu, Nijar ma haka, kuma zan je Ghana nan bad a jimawa ba. kuma ga Botswana da Mauritius. A matsayinmu na shugabannin yaki da almundahana na kasashen rainon Ingila a Afirka muna da hadin gwiwa da kasashe da dama a Afirka. Kuma a wajen Afirka muna da hadin gwiwa da kasashe da dama. Kuma muna aiki da hukumomin NCA da FBI da sauransu. Wasu lokuta wajibi ne ka yi taka-tsantsan wajen bayyana abubuwan da kuke yi, amma muna da hadin gwiwa da hukumomi da dama wajen yaki da almundahana.

 

To yaya batun bankuna, domin idan aka lura za a ga akwai batutuwa a bankunan. Domin jiya wata da aka zaba don nada ta a Hukumar ICPC, ta yi da’awar cewa wata fallasa da ta yi ne ta jawo ake kokarin hana ta kasancewar a hukumar…

Eh, muna bincikar batun.

 

Ta fadi yadda aka yi…

Ta fada a jaridu? Eh ta yi korafi. Ita ce ta kawo korafi a kan batun, don haka muna bincike a kai. Babban lamari ne. Domin wadansu masu bankunan su ne suke jagorantar a cire bangaren bincike da sanya ido kan harkokin kudi domin idan aka yi haka zai zamo baa bin da za a tuhume su da shi ke nan. Ana hada baki da wadansu masu bakuna a bude asusu ta yadda babu wanda zai sani daga su sai mai asusun. Hatta Hukumar NDIC mai kula da bankuna in jami’anta sun je ba za su sani ba. Saboda suna da takardun da suke gabatarwa nau’i biyu: ta gaskiya da ta jabu.  Idan Hukumar EFCC ko NDIC ko Babban Banki ya zo sai su nuna musu wadda suke so. To mu ma muna da hanyoyinmu na gano abubuwa. Wasu daga cikin bankunan masu almundahanar kudade ne suka mallake su.

 

To yaya kuke yi da batun shirin fallasa da ake kira ‘hura usur’ da aka bullo da shi?

Muna aiki da shi, sai dai wasu lokuta mutane suna jawo a ji kunya. Domin haka dole a yi taka-tsantsan da shirin.

 

Wane kalubale kuke fuskanta wajen kwato kudaden da aka kai kasashen waje?

Ana samun ci gaba idan aka lura da abin da muke da shi a baya, kasashen da lamarin ya shafa suna bayar da hadin kai gwarwagdo, sun yarda cewa za su yarda su dawo da kudin. Wasu lokuta ba su son su ce nawa aka sace mana. Ina jin mamaki wani ya sace Dala miliyan 200 yaya za a yi a cimma matsaya kan dawo da Dala miliyan 200, ba abu ne mai sauki ba, amma sun amince za su dawo mana da kudadenmu.

Wannan yaki da muke yi da cin hanci da rashawa, aiki ne da ke kan kowa kuma kuna yi ne ga kasa ba ni ba, don haka ko Magu yana nan ko ba ya nan ya kamata a ci gaba da shi don amfanin kasar nan.

 Abin da nake so shi ne kada kafafen watsa labarai su bari a yi amfani da su wajen lalata kasar nan. Dukanmu muna da hakki a kanmu, Allah Ya hallice mu ne da manufa, kuma bai yi kuskure ba wajen hakan. Mu tabbatar mun yi abin da yake daidai, domin idan ba mu yi gyara a wannan lokaci ba, to mu manta da batun gyara.

Kiraye-kirayen da ta da kura da ake yi a kasar nan, duk ba gaskiya ba ne, ba da gaske ake yi ba. Wadanda suke daure wa wadannan kiraye-kiraye da tayar da kura, su ne wadanda suka tafka barna suka sace dukiyar kasar nan.  

 Wadanne kiraye-kiraye ko tayar da kura?

Kiraye-kirayen da ake yi na neman raba kasa da makamantansu. Abin da nake cewa dukanmu muna da nauyi a kanmu na mu tabbatar da kasar nan ta kasance a dunkule. Ba na fi ku sani ba ne, ku ’yan jarida ne, ban fi ku sani ba. Ina tunatarwa ce kawai, cewa ya kamata mu kare martabar kasar nan. Wannan nauyi ne da ke kanmu duka.