Lokacin Idin Maulidi ya sake zagayowa. Rana ce da aka haifi fiyayyen halitta – Annabi Muhammad (SAW). Ana bikin ne a kowace ranar 12 ga watan Rabiul Awwal na shekarar Musulunci, bikin na bana ya zo daidai da ranar Lahadi 10 ga Nuwamba 2019. Gwamnatin Tarayya ta bayar da hutun Maulidin a ranar Litinin da ta gabata tare da kiran Musulmin da sauran jama’ar kasar nan da su yi wa Najeriya addu’o’in zaman lafiya da hadin kai tare da ci gaban kasa. Gwamnonin jihohi da manyan kasar nan su ba a bar su a baya wajen irin wannan kira. Daga cikin abubuwan da ke sahun gaba da addinin Musulunci yake koyarwa shi ne, imani da Allah da kuma sadaukarwa tare da hidima ga al’umma. Sura ta 2 aya ta 177 ta yi bayani karara game da rukunonin imani kamar haka: Yin imani da Allah da Ranar Karshe, imani da mala’iku, imani da littatafai da manzanni, sai kuma umarnin da ciyarwa daga dukiyarka ga ’yan uwa da sauran dangi da marayu da mabukaci da matafiyi da miskinai da kuma ’yantar da bayi; sa’annan kuma da tsayar da Sallah da yawaita sadaka da cika alkawura da kuma jurewa tare da hakuri a lokacin tsanani da jarrabawa.
A wani wajen kuma har ila yau, Kur’ani ya horar kan hidima ga iyaye ba tare da la’akari da addininsu ba, tare da kyautata wa makwabta da marasa lafiya da tsofaffi da tsirarun rukunin jama’a da umarni da aikata kyawawan ayyuka tare da nusarwa kan kaurace wa munana. Kada a ci zarafin ko take hakkin wani kuma babu hujjar cutar da shi. An ruwaito Annabi Muhammad (SAW) yana cewa: “Mutum ba ya daiImani idan dai ya cika cikinsa; alhali makwabcinsa kuma yana cikin yunwa.” Dukkan wadannan kyawawan halaye da dabi’u sun kasance halayensa ne (Sallallahu alaihi wasallam). A takaice dai rayuwarsa gaba daya ta tafi ne kan haka. Al’ummar Musulmi mai cike da adalci da daidaito da ya kafa a lokacinsa ta kasance abar misali da har yanzu babu kamarta. Ya tabbata, kamar yadda aka ruwaito a ganiyar lokacin mace za ta yi kayan zinare ta dora a kanta tana tafiya tun daga birnin Madina har ta dangana da birnin Makka – tafiya mai nisan fiye da Mil 300 – ba tare da wani ya hantare ta ba.
Wannan shi ne mutumin da ake Idin tunawa da rayuwarsa, a ranar Maulidi. Sai dai Kash! Akwai takaici matuka lura da irin babban gibin dabbaka irin wadannan kyawawan dabi’u da wannan babban Manzo ya koyar a Najeriyarmu ta yau. A yau rashin tsaro tare da ayyukan tarzoma sun yi wa kasar daurin huhun goro. Cin hanci ya zama ruwan dare, wanda ummul haba’isansa shi ne rashin gaskiya da adalci daga manya ko ’yan bokon kasar nan. Wadanda ake mulkinsu na nuna halin ko oho sakamakon fusatarsu da irin yadda tabarbarewar al’amura suka yawaita. Kishin kasa, a wajensu ba a bakin komai yake ba – yayin da suke fadi-tashin neman abin rayuwa ta kowace hanya – walau ta halal ko haram. Koda yake, ba wai kawai a Najeriya ce ake samun karancin koyi da kyawawan halayen wannan babban Manzo (SAW) ba, a’a abin ya zama kusan ruwan dare ne game-duniya a halin yanzu. Yayin da wadansu ke rayuwa ta nuna isa da izza wadansu kuma na kwanciya da yunwa tare da rashin muhalli. Ga kuma kashin dankali na manyan kasashe kan masu tasowa inda suke danne kananan ta hanyar rashin daidaito a tsarin kasuwancin duniya tare da saka kananan kasashen cikin tarkon basussuka masu ruwa na fitar hankali.
Lokacin Idin Maulidi ba wai lokaci ne na fantamawa da shagali ba, a’a lokaci ne na nuna jinkai da tausayi tare da sadaukarwa. Don haka muke kira da babbar murya ba wai kawai ga Musulmin Najeriya ba; har ma da sauran ’yan uwansu a duniya su tsaya su yi nazari game da irin manyan kalubalen da ke fuskantar duniya, kana su sassauto tare da kyautata imaninsu ga Ubangiji wajen rungumar hakikanin kyawawan dabi’u da sadaukarwa da kuma hakuri da nuna ’yan uwantaka. Ba kawai ’yan Najeriya za su yi aiki da musayar miyau wajen shawo kan bambance bambancensu ba ne, kamata ya yi su fatali da duk wani tunzuri da tashin hankali da wadansu marasa kishin kasa za su yi sanya su ba – wanda daga karshe ba zai haifar da da mai ido ba. Ta haka ne kyawawan darussan da Maulidin ya koyar za su zama masu amfani. Wani muhimmin abu, shi ne babban nauyin samar da zaman lafiya da ci gaban kasa ya rataya ne kacokan a wuyan gwamnatoci a dukkan matakai. Yanayin yadda gwamnati ke tafiyar da kasa shi ne ma’aunin da zai tantance jin dadin al’ummar kasar. Don haka shugabanni a dukkan matakai kamata ya yi su tashi tsaye wajen sauke wannan nauyi da ke kansu ta hanyar gina al’umma tagari, mai adalci da daidaito. Ta haka ne kawai za a iya samar da wadannan ababuwa. Muna yi wa Musulmi masu karanta jaridarmu Barka da Idin Maulidi.