Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa gomman ma’aikatun Gwamnatin Tarayya suna yin aiki ba tare da shugabannin ba ko kuma hukumar gudanarwa tsawon shekaru biyu kenan.
Shugaba Muhammadu Buhari ya rushe kwamitin gudanarwar hukumomin a ranar 16 ga watan Julin shekarar 2015 amma bayan watanni biyu sai ya kafa kwamiti karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnati, Injiniya Babachir Lawal ya sake kafa su.
Tun wannan lokacin ba a sake kafa kwamitin gudanarwar ba inda hakan kamar yadda wata majiya ta ce ya yi wa harkokin tafiyar da hukumomin illa.