Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Kasa ta ce za ta hada gwiwa da Hukumar NCC domin cire kimanin matasa miliyan 10 daga talauci.
Mista Ramon Balogun, Mataimakin Daraktan Sadarwa na Ma’aikatar ne ya bayyana haka a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja.
Balogun ya ce Minsitan Matasa da Wasanni, Mista Sunday Dare ne ya bayyana haka a lokacin karrama shi da Hukumar NCC ta yi.
Kamfani Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Dare ya taba zama kwamishina a hukumar.
Ya ce ma’aikatar za ta yi aiki da Hukumar NCC domin samar da aiki ga matasa ta wajen ba matasa ilimi da horo ta hanyar koyar da su ilimin kwamfuta.
“Akwai wasu hanyoyin sadarwa na zamani da za su taimaka wajen gina matasa domin dogaro da kai da fara kasuwanci don tunanin ci gaba.”
Ya bayyana godiya ta musamma ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya bashi dama ganin ya cancanci rike ma’aikatar.
Shugaban Hukumar NCC Farfesa Garba Dambatta ne ya mika wa ministan kambun karramawa a wajen taron.