✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan wutar lantarki sun janye yajin aikin da suka fara

Sun janye yajin aikin ne bayan tattaunawa da Ministan Kwadago

Ma’aikatan wutar lantarki na Najeriya sun janye yajin aikin da suka tsunduma ranar Laraba wanda ya kai ga jefa ilahirin kasar cikin duhu.

Kungiyoyin ma’aikatan lantarkin dai da suka hada da NUEE da SSAEC sun amince su janye yajin aikin ne bayan wani zaman tattaunawa da suka yi da Ministan Kwadago, Chris Ngige a ranar Laraba.

Ministan dai ya kira ma’aikatan ne zaman tattaunawa na gaggawa tsakaninsu da Gwamnatin Tarayya don a magance batutuwan da suka kai ga shiga yajin aikin.

Batutuwan da suka kai su ga shiga yajin aikin dai sun hada da kin bin doka wajen yi wa ma’aikata karin girma, nuna musu wariya a ofishin Shugabar Ma’aikata ta Kasa da kuma kun biyan tsofaffin ma’aikatan hukumar PHCN kamar yadda aka yi a yarjejeniyar 2019.

Da yake zantawa da ’yan jarida jim kadan da kammala tattaunawar da ta dauki kusa awa hudu, Babban Sakataren NUEE, Kwamared Joe Ajaero, ya ce an umarce su da su janye yajin aikin.

Sakataren wanda ya bayyana fatansu na ganin gwamnati ta yi abin da ya dace, ya kuma ce batutuwan da suka kai su ga shiga yajin aikin sun dade suna jeka-dawo a kansu.

Ya ce za su jinkirta da yajin aikin ma tsawon mako kamar yadda gwamnati ta amince yayin tattaunawar domin ba ta damar cika alkawuran da ta dauka.

Shi kuwa a nasa bangaren, Minista Ngige ya ce an kafa wani kwamiti mai bangarori biyu da zai ba damar duba batutuwan da nufin magance su, sannan ya mika rahotonsa nan da mako biyun.

Kwamitin dai zai kasance a karkashin jagorancin Minista a Ma’aikatar Lantarki, Jeddy Agba, sai Babban Sakatare a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya da na Ofishin Shugaban Ma’aikata na Tarayya da na Ma’aikatar Kwadago da wakili daga Hukumar Cefanar da Kadarorin Gwamnati (BPE) da kuma wakilai biyu daga NUEE da SSAEC.