Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Kasa (JUSUN), reshen Jihar Kano, ta shirya shiga yajin aiki daga ranar 6 ga Afrilun 2021.
Hakan na dauke ne a sanarwa da Shugaban JUSUN, reshen Jihar Kano, Mukhtar Rabiu Lawan ya fitar a ranar Litinin.
- A shirye muke a kashe mu kan ceto ’ya’yanmu —Iyayen dalibai ga El-Rufai
- An kama tsofaffin jami’an soji 10 a Turkiyya saboda sukar gwamnati
- Caca: Yadda N50 ta yi sanadiyyar kisan mutum 3
- An fara yi wa maniyyata aikin Hajji rigakafin COVID-19
“Wannan mataki ya biyo bayan umarnin da uwar kungiya ta kasa ta bayar. Don haka za mu tafi yajin aiki tare da kulle dukkanin ma’aikatun shari’a da kuma kotuna,” a cewar Lawan.
Kazalika, shugaban ya ce reshen Kano na JUSUN na umartar dukkan mambobinta da su rufe kotuna da ma’aikatun shari’a na jihar har sai an samu karin bayani daga uwar kungiyar ta kasa.
Tun a ranar 1 ga watan Afrilyu, uwar kungiyar JUSUN ta kasa ta ba da umarnin shiga yayin aikin.