✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Ma’aikatan shari’a sun garkame kotuna bayan fara yajin aiki

Ma’akatan suna yajin aikin ne saboda Gwamnati ta ki tabbatar da ’yancin cin gashin kai ga bangaren shari’a

Yajin aikin da Kungiyar Ma’aikatan Shari’a na Najeriya (JUSUN) suka tsunduma ranar Talata ya kassara harkokin shari’a a sassa da dama na kasar bayan sun garkame kotuna.

Ma’akatan suna yajin aikin ne saboda yin kememen da Gwamnatin Tarayya ta yi wajen tabbatar da ’yancin cin gashin kai ga bangaren shari’a ta fannin samar musu da kudade.

A Jihar Kano kamar sauran jihohin Najeriya da dama, akasarin kotunan da wakilinmu ya ziyarta a Sakatariyar Audu Bako ya tarar da dukkansu a rufe sakamakon yajin aikin.

Da yake tattaunawa da Aminiya, Sakataren JUSUN reshen jihar ta Kano, Kwamared Sulaiman Aliyu ya ce sun yanke shawarar garkame kotunan ne saboda bin umarnin uwar kungiyarsu ta kasa.

Ya ce suna yajin aikin ne da nufin tursasa wa gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma tun shekarar 2013 amma Gwamnoni suka yi biris wajen aiwatarwa.

“Ko a kwanan nan sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan dokar da ta ba da umarnin a biya mu hakkokinmu amma suka yi kunnen uwar shegu,” inji shi.

Sai dai yawancin ’yan Najeriya ba su da masaniya a kan yajin aikin har sai lokacin da suka je harabar kotunan amma suka tarar da su a rufe.

Alhaji Ibrahim Muhammad wani magidancin ne da ya je kotun da nufin ci gaba da sauraron wata kara da ta shafi ’yarsa amma ya tarar da kotun a rufe.

Ya ce kusan wata daya ke nan ya shafe yana jiran ranar sauraron karar kafin yajin aikin ya zo ya yi masa yankar kauna.

“Ban san yau za a fara yajin aikin ba na garzayo kotu saboda yau aka tsayar domin sauraron kararmu.

“Lokacin da na zo na tarar da wani lauya wanda ya shaida min cewa JUSUN sun fara yajin aiki,” inji shi.

Ya yi kira ga gwamnati da kungiyar ma’aikatan kotunan da su sasanta tsakaninsu kasancewar kotuna ne kadai hanyoyin samar da maslaha ga al’umma.

Kazalika, hatta masu sana’o’i a kewayen kotunan su ma sun fuskanci tasgaro bayan da ma’aikatan suka umarce su da su bar wurin.