✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan NAFDAC sun shiga yajin aiki

Ma’aikatan Hukumar NAFDAC sun fara yajin aikin gargadi na kwana bakwai

Ma’aikatan Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) sun fara yajin aikin gargadi na kwana bakwai.

Jami’an na bangaren lafiya a NAFDAC sun fara yajin aikin gargadin ne a ranar Alhamis domin matsa wa gwamnati ta biya su bukatunsu na kudin karin girma, a yi musu karin alawus ya dace da sabon mafi karancin albashi, biyan kudaden sallama da kuma samun horo.

Mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan, Kwamared Ejor Michael, ya ce “Muna neman a biya bashin da ma’akata suke bi na kudin karin girma na shekarar 2018 da 2019 da 2020.

“Yanzu shekara 10 ba a yi karin kudin alawus din aiki ba, alhali yana karuwa idan aka yi karin albashi. Saboda haka muke bukatar a kara shi ya dace da karin da aka yi na sabon mafi karancin albashi.

“Muna tir da dakatar da biyan kudaden sallama ga wadanda suka yi ritaya. Kwamitin daraktocin NAFDAC ya amince a biya rika biyan su kamar yadda yake kunshe a dokar aikin NAFDAC.

“Muna neman bukatar a ci gaba da biyan alawus din ga wadanda suka cancanta ba tare da bata lokaci ba.

“NAFDAC tana fakewa da COVID-19 tana kin tura ma’aikata samun horo, alhali an ci gaba tura ma’aikatan sauran hukumomin gwamnati samun horo. Saboda haka muke bukatar nan take a fara tura mambobinmu zuwa samun horo,” inji sanarwar.

Sun kuma bukaci a gyara bambancin da ake nunawa wurin biyan tallafin COVID-19.

“Ba mu amince da bambancin da NAFDAC ke nunawa wurin biyan tallafin COVID-19 ba, yadda take biyan wani kaso ko ma ta ki biyan wasu ma’aikatan,” inji sanarwar.

Ta kuma bukaci hukumar da ta yi koyi da sauran hukumomin gwamnati wajen biyan alawus mai gwabi ga ma’aikatan da suka gudanar da ayyukan sayar da rai.

Sun kuma koka bisa mawuyacin halin da ofisoshin hukumar suke ciki musamman a Isolo, Legas, inda suka ce kananan ma’aikata kamar direbobi da masu shara ke amfani kudadensu domin tabbatar da ganin aiki bai tsaya ba.

Uwa uba ba a biya ma’aikata kudadensu, sai an dauki tsawon lokaci, ba tare da wani bayani ko kwakkwaran dalili ba.